Cristiano Ronaldo ya yi watsi da zargin yin fyade

Lokacin karatu: Minti 2

Shahararren dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya yi watsi da zargin cewa ya yi wa wata mata fyade a wani otel a Amurka kimanin shekara goma da suka gabata.

Tsohon dan wasan gaban Real Madrid din, mai shekara 33, ya ce hankalinsa a kwance yake kan duk wani bincike da za a gudanar a kansa kan zargin cewa ya far wa Kathryn Mayorga a wani daki a otel din Las Vegas a shekarar 2009.

Ya yi maganar ne gabanin lauyoyinta su gabatar da wani taron manema labarai a ranar Laraba.

A can baya dai ya ce zargin, wanda wata mujalla ta kasar Jamus Der Spiegel ta fara wallafawa labarin "kanzon kurege ne."

A ranar Laraba ne ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Twitter:

Mujallar Der Spiegel ta ce Mayorga, mai shekara 34, ta shigar da korafi ga ofishin 'yan sanda na Las Vegas jim kadan bayan da lamarin da take zargin ya faru.

Amma shakara guda bayan wannan, an ruwaito cewa sun sasanta ita da Ronaldon ba tare da sa bakin kotu ba, inda ya ba ta dala 375,000 da yarjejeniyar cewa ba za ta fallasa batun ba.

A yanzu haka lauyoyinta suna so su wargaza waccar yarjejeniyar ta farko.

A ranar Talata 'yan sandan Las Vegas sun tabbatar da cewa a baya sun yi bincike kan korafin a watan Yunin 2009, amma sun kara da cewa babu wanda suke zargi a lamarin.

Wata sanarwa ta ce: "Duk lokacin da aka dauka na shigar da korafin, matar ba ta sanar da 'yan sanda wajen da abin ya faru ba."

"A watan Satumbar 2018 ne aka sake waiwayar shari'ar kuma jami'anmu suna bin diddigin bayanan da aka samar," a cewar sanarwar.

Lauyoyin Ronaldo a baya sun ce za su shigar da karar Mujallar Der Spiegel kan labarin da ta ruwaito.