Jiragen soji sun yi hatsari a tsaunukan Katampe a Abuja

Asalin hoton, NAF
Rundunar Sojin saman Najeriya ta sanar da rasuwar daya daga cikin matukan jiragen da su ka yi hatsari a lokacin da su ke shawagi a unguwar Katampe da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Rundunar ta tabbatar da faduwar jiragenta biyu a unguwar mai tsaunuka a ranar Juma'a da misalin 11.30.
Jiragen biyu sun fadi ne bayan da suka gogi juna, a yayin wani atisaye da suke yi a wani bangare na shire-shireyen bukukuwan ranar samun 'yancin Najeriya wanda za a yi ranar Litinin mai zuwa.
Abokin aikinmu Abdou Halilou da abun ya faru a gabansa, ya ce ya ga faduwar jiragen inda kuma daya ya kama da wuta nan take.
Ya ce jiragen uku ne ke tafiya a jere, ya kuma ga faduwar daya a tsaunin Katampe.
"Amma kafin jirgin ya fado, daya daga cikin mutanen da ke cikin jirgin ya diro da lemar jirgi sannan jirgin ya kama da wuta," a cewar Abdou.

Wadanda suka shaida lamarin dai sun ce sun ga mutum biyu da suka fado daga cikin jirgin sun kama da wuta.
Da farko dai rundunar sojin saman ta fitar da wata sanarwa inda ta ce babu wanda ya rasa ransa, "amma za mu sanar da krin bayani nan gaba."
Daga baya ne ta fitar da sanarwar cewa daya daga cikin mutakan jirgin ya rasu bayan da ya diro daga jirgin kuma ya bugu da kasa. Ya samu raunuka kuma an kai shi asibiti inda a nan ne ya rasu.
Tun a makon jiya ne jiragen su ka fara yawo a babban birnin, inda a ke tunanin su na atisayen bikin ranar samun 'yancin Najeriya ne wanda za a yi ranar Litinin mai zuwa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A ranar 17 ga watan Satumba ne rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da wata sanarwa a shafinta na Twitter cewa:
"Rundunar sojin sama za ta yi wani atisaye cikin shirye-shiryen bikin samun 'yancin kan kasar na shekara 58.
"Don haka jiragen rundunar za su dinga shawagi kasa-kasa daga nan har ranar 2 ga watan Oktobar 2018.
Ana umartar mutane su ci gaba da harkokinsu yadda suka saba kar su tsorata."

Tsaunukan Katampe dai na kan babban titin fita garin Abuja, wanda a ka fi sani da Kubwa Expressway.

Asalin hoton, NAF











