Omisore ya sha alwashin mara wa APC baya a karashen zaben Osun

PDP da APC
Lokacin karatu: Minti 3

Dan takaran jam'iyyar SDP, a zaben gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore, ya ce jam'iyyar APC zai mara wa baya a karashen zaben da za a yi ranar Alhamis.

Omisore ya yi wannan maganar ne a wani taron manema labarai da ya yi a Ile Ife.

Ya ce abin da ya sa tsayar da wannan shawara shi ne yadda manufofin jam'iyyar APC suka zo daya da jam'iyyarsa.

Tun bayan da hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta ce ba a kammala zaben gwamnan jihar Osun ba, hankulan mutane suka koma kan mazabu bakwai din da za a sake zabe.

Uku daga cikin mazabun na karamar hukumar Orolu yayin da daya ke karamar hukumar Osogbo.

Bugu da kari, akwai mazabu uku a kananan hukumomin Ife ta Kudu da Ife ta Arewa, inda ake ganin dan takarar jam'iyyar SDP a zaben, Iyiola Omisore, ya fi magoya baya.

Kuma tun lokacin da hukumar INEC ta ba da sanarwar cewar za a karasa zabe a wadannan mazabun ranar 27 ga watan Satumba ne dai jam'iyyun PDP da APC suka fara zawarcin dan takarar na jam'iyyar SDP.

INEC dai ta fitar da sanarwar sake zabe a mazabu bakwai din ne ranar 23 ga watan Satumba, kuma washe gari, 24 ga wata, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya kai wa Mista Omisore ziyara.

Yayin ziyarar, Mista Saraki ya nemi dan takarar SDP din ya goya wa dan takarar jam'iyyarsa, Nurudeen Ademola Adeleke, baya a zaben na ranar Alhamis.

A wani sakon Twitter da ya wallafa bayan ziyarar, Bukola Saraki ya gode wa Omisore da irin tarbar da ya yi masa.

Shi kuwa Omisore ya wallafa hotunan ziyarar ta Saraki ne da maudu'in #OsunDecides2018 da kuma #goodgovernanceinosunstate.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Rahotanni dai sun ce ya shaida wa Saraki cewar shi zai goyi bayan duk wani dan takarar da zai biya albashi da kudin fansho a kan kari da kuma samar da gwamnati mai nagarta.

Cikin sa'o'i 24 bayan ganawa da Saraki kuma, Mista Omisore ya karbi tawagar jam'iyyar APC wadda gwamnan jihar Ekiti mai jiran gado, Kayode Fayemi, ya jagoranta.

A hoton da ya wallafa na ganawarsa da Mista Fayemi, Omisore ya sake ambatar madu'in #OsunDecides2018 da kuma #goodgovernanceinosunstate.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Me yasa jam'iyyun suka fi damuwa da Omisore ne?

A cikin mazabu bakwai din da za a sake zabe, mazabu ukun da Omisore ya fi karfi ne ke da kuri'unsu suka fi yawa.

Jimillar masu zabe a wadannan mazabu da ke kananan hukumomin Ife ta Kudu da Ife ta Arewa shi ne 1,667.

Akwai mazabu uku da za a sake zabe a karamar hukumar Orolu, kuma suna da jimillar masu zabe 947.

Nurudeen Adeleke na jam'iyyar PDP (a dama) da Goyega Adeoti na APC (a hagu)

Asalin hoton, Twitter/@Aregbesola Twitter/ @Isiakadeleke

Bayanan hoto, Nurudeen Adeleke na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba bayan ya samu kuri'u 254, 698 yayin da Goyega Adeoti ke bi masa baya da kuri'u 254,345

Mazaba daya da sake zabe a karamar hukumar Osogbo tana da masu zabe 884.

Wannan shi ya sa hakulan jam'iyyun PDP da APC suka karkata zuwa ga dan takarar SDP din.

Tasirin mataimakin Dogara

Bayan kanan hukumomin Ife ta Kudu da Ife ta Arewa, karamar hukumar da ta fi yawan kuri'u a zaben da za a sake ranar Alhamis ita ce karamar hukumar Orolu.

Kuma wannan wuri ne da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Yusuf Lasun, ya fi samun goyon baya.

Yusuf Lasun
Bayanan hoto, Yusuf Lasun ya ce alakarsa da Dogara ba ta shafi goyon bayansa ga jam'iyyar APC ba

Kuma kwannan nan ne Yakubu Dogara, wanda ke aiki tare da Lasun a Majalisar Wakilai, ya sauya sheka zuwa PDP.

Sai dai a ranar Asabar Lasun din ya tabbatar wa BBC cewa shi yana tare da jam'iyyarsa duk da cewa abokin aikinsa ya sauya sheka.