Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun samu rokokin zamani duk da kokarin Isra'ila na hana mu - Hezbollah
Shugaban kungiyar Hezbollah ta Lebanon ya ce sun samu makamai na zamani duk da kokarin Isra'ila na hana ta yin hakan.
Hassan Nasrallah ya shaida wa magoya bayansa cewar kokarin Isra'ila na katse wa kungiyar hanyoyin samun makamanta ba za su yi tasiri ba.
Isra'ila dai ta sha kai hare hare ta sama a Syria da nufin kassara duk wani yunkuri na Iran wajen samar da makamai na zamani ga abokan kawancenta, wato kungiyar ta Hezbullah.
Ya ce: "duk wani mataki da kuka dauka na datse hanyoyin, yanzu zance ya kare, kuma kungiyarmu ta mallaki makaman roka na zamani, da wadanda ba su kai su inganci ba, dama fasahar kera sauran makamai."
Hassan Nasrallah ya ce "bakin alkalami ya bushe."
Duk da yana ikirarin kungiyar ta Hezbullah ta mallaki makamai masu linzami, bai fito da wasu shaidu dake nuna hakan ba.
Mallakar makaman roka masu zama, da za a iya kai hari da su, kan inda duk ake so zai sa Hezbollah kara zama babbar barazana ga Isra'ila idan wani yaki ya kara barkewa tsakaninsu.
Idan Isra'ila ta daura damarar yaki da Lebanon, to kuwa Isra'ilar za ta fuskanci wata makoma, da wani yanayi, wanda ba ta taba zatonsa ba ko da da rana guda.