An kashe ma'aikaciyar Red Cross a Najeriya

ICRD

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar bayar da agaji ta The International Committee of the Red Cross ta bayyana matukar kaduwarta bisa kashe ma'aikaciyarta da aka yi a arewacin Najeriya.

'Yan bindigar da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne suka sace Saifura Hussaini Ahmed Khorsa, wacce ma'aikaciyar jinya ce da abokan aikin ta a garin Rann na jihar Borno a watan Maris.

Sanarwar da mai magana da yawun Red Cross, Eleojo Esther Akpa, ta aike wa manema labarai ta yi kira ga 'yan bindigar su saki sauran ma'aikatan biyu - Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha - da suke hannunsu.

Red Cross ta ambato babban jami'inta da ke Abuja Eloi Fillion na cewa, "Mun yi matukar kaduwa kan kisan da aka yi wa abokiyar aikinmu Saifura. Wannan baiwar Allah ta tafi Rann domin ta bayar da taimako ga mabukata.

"Muna yin jaje ga 'yan uwa da iyayenta a wannan mawuyacin hali da suka tsinci kan su a ciki."

Kungiyar ta ce ma'aikatanta ba su da hannu a yakin da ake yi, tana mai cewa ma'aikatan jinya da ungozoma ne.

Ita dai Saifura, mai shekara 25, matar aure ce mai 'ya'ya biyu wacce ke aikin jinya.

Lokacin da aka sace su batun ya ja hankalin 'yan Najeriya inda suka rika kira a sake ta.

Red Cross ta ce tun da aka sace ma'aikatan nata wata shida da suka gabata take kokarin ganin an sake su, tana mai cewa za ta yi bakin iyakar ta wurin ganin an saki Hauwa da Alice ba tare da ko da kwarzane ba.