Tarayyar Turai: Za a daina rage agogo a lokacin sanyi.

Clock gears

Asalin hoton, Eyewire inc.

Hukumar Tarayyar Turai ta fitar da wani sabon tsari da zai kawo karshen yadda ake sauya agogo a lokutan zafi da na sanyi a fadin nahiyar.

Hukumar ta gano cewa yawancin 'yan kasashen Turai ba su goyi bayan cigaba da tsarin na kara agogo gaba da sa'a guda a lokutan sanyi, da kuma rage shi da sa'a guda a lokuta zafi ba.

Shugaban hukumar Jean-Claude Juncker ya ce miliyoyin 'yan kasashen Turai na so a rika amfani da lokaci na bai daya daga lokacin sanyi zuwa lokacin zafi.

Ya kuma ce yana da karfin gwuiwar abin da zai faru kenan nan ba da jimawa ba.

Amma kafin hukumar ta aiwatar da wannan sauyin, sai dukkan mambobin tarayyar Turai 28 sun amince da matakin.

Wani kudurin majalisar Tarayyar Turai ya bayyana abin da ya kira "fa'idar amfani da lokaci na bai aya a fadin tarayyar ta Turai".

Birtaniya na cikin kasashen 28 da dole sai sun amince da sauyin kafin a gudanar da shi, amma kuma za ta fice daga Tarayyar nan da karshen watan Mayun 2019, wanda ke nufin dukkan sauye-sauyen da za a gudanar su auku kafin ficewar ta kenan.

Humumar ta Tarayyar Turai ta yi gargadin cewa dukkan sauye-sauyen da ba na bai daya ne ba, za su kawo cikas matuka ga tattalin arzin kasashen Turai.

A wani shirin jin ra'ayin jama'a da aka gudanar, an gano cewa kashi 84 cikin 100 na wadanda aka tambaya sun nemi da a daina sauya lokutan agogo da akan yi na tsawon sa'a guda.

A halin yanzu a akwai yankuna guda uku na Turai da ke amfani da nasu tsarin na auna lokaci.

  • Kasashen Birtaniya Ireland da Portugal na amfani ne da tsarin GMT
  • Kasashe 17 da kuwa na amfani ne da tsarin Central European Time wanda suke kara sa'a guda ga lokacin GMT.
  • Kasashe takwas kuma na amfani ne da tsarin Eastern European Time mai kara sa'a biyu ga lokacin GMT.