Atiku ya ce ma'aikaci ke motsa jiki

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Twitter/@Atiku

Bayanan hoto, Atiku ya ce ba motsa jiki ne ma'unin iya mulki ba
Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari shagube kan ikirarin da ya yi cewa motsa jikin da ya yi ya ba shi damar kimtsawa domin fuskantar zaben 2019.

Ranar Talata ne dai shugaban kasar ya halarci filin sallar Idi a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, sannan ya yi tafiyar mita 800 a kasa daga masallacin zuwa gidansa bayan an sauko daga Idi.

Daga bisani ne mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya fitar da sanarwar da ke cewa "takawar da Shugaba Buhari ya yi a kasa daga masallaci zuwa, cike da sowa da tafin magoya baya, ya nuna cewa duk wanda yake shakkun koshin lafiyar shugaban ya kamata ya sake nazari."

Wasu na gani fadar shugaban kasar ta yi wannan kalami ne domin yin raddi ga masu cewa Shugaba Buhari ba shi da koshin lafiyar sake tsayawa takara a zaben 2019.

Buhari da 'yan rakiyarsa

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Bayanan hoto, Buhari ya kwashe sama da kwana 100 a London yana jinya a bara

'Ina motsa jiki a ko da yaushe'

Sai dai a wani sakon Twitter da Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa inda ake ganin tamkar shagube ga kalaman fadar shugaban Najeriya, ya ce motsa jiki ba shi ne ma'unin iya mulki ba.

"A ko da yaushe ina yin sassarfa da motsa jiki na tsawon mil daya amma ina ganin bai dace hakan ya zama ma'aunin da zan yi amfani da shi wurin neman kuri'ar 'yan Najeriya ba. Ina son jam'iyyata, PDP da kuma 'yan Najeriya su zabe ni saboda na yi aiki ba motsa jiki ba. Ba zan yi tafitar da za ta zama maras amfani ba."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

line

Sau biyu dai Shugaba Muhammadu Buhari yana tafiya jinya London tun da ya zama shugaban kasa a 2015.

Hakan ya sa 'yan kasar da dama na ganin shugaban, mai shekara 75, ba shi da cikakkiyar koshin lafiyar sake yin mulki a wa'adi na biyu.

Sai dai fadarsa da ma mukarrabansa sun sha cewa Shugaba Buhari ya murmure sosai kuma a shirye yake ya sake jagorantar kasar.

Shugaba Buhari ya ce bai taba fama da rashin lafiya irin wannan ba

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya ce bai taba fama da rashin lafiya irin ta wancan lokacin ba

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"

5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"

28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba

3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London

Ga wasu karin labarai da za ku so karanatawa: