Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An nada El-Rufai sarautar Garkuwan Talakawa
Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce an nada gwamnan jihar a matsayin Garkuwan Talakawa.
Wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ya ce Masarautar Jama'a ta nada Gwamna El-Rufai a kan wannan matsayi.
Wasu da ke bibiyar shafin sun yi tsokaci a kan nadin, inda suke kira a gare shi da ya aiwatar da manufofi da za su kawo ci gaban talakawa.
"Ina taya ka murna. Ina kuma addu'a da fatan ganin wannan mukami da aka ba ka ya yi maka kaimi wurin aiwatar da shirye-shiryen da za su kyautata rayuwar talakawa", in ji Dr Tim Zakwai Auta
Gwamna El-rufai dai ya yi kaurin suna wurin jawo ce-ce-ku-ce, sanna ya sha aiwatar da manufofin da wasu ke ganin sun saba da tunanin talakawa.
Wasu daga cikin manyan babubuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce a mulkinsa su ne rushe-rushen gidaje da kuma wasu gine-gine, ko da yake ya sha cewa yana yi ne domin tabbatar da dokokin gine-gine.
Kazalika Gwamna El-Rufai ya kori malaman makarantun firamare da sakandare da kuma cire masu rike da sarautun gargajiya da dama.
Sai dai ya ce ya kori malaman ne domin ba su cika ka'idojin zama malamai ba, sannan ya rusa masarautun ne domin an kirkiro su ne ba bisa ka'ida ba.