Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jarumin fina-finan Kannywood ya rasu
Allah ya yi wa jarumin fina-finan Kannywood Ayuba Dahiru wanda aka fi sani da Tandu rasuwa.
Marigayin ya rasu ne ranar Lahadi da safe a birnin Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
Abokin sana'arsa, Malam falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa "Ayuba (Tandu) ya rasu ne bayan ya yi fama da zazzabi na kwana biyu. Muna addu'ar Allah ya yi masa gafara."
Tandu ya fito a fina-finan barkwanci da dama wadanda suka hada da "Auren Manga" da "Gobarar Titi".
Ya bar mata uku da 'ya'ya tara.