'Labaran kanzon kurege na kashe kasa' - al Sisi

An fara wani kamfe a kafofin watsa labaran kasar Masar domin yaki da illar baza jita-jita da labaran kanzon kurege ta shafukan sada zumunta.

Wannan matakin ya zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya gargadi 'yan kasar game da wannan halayyar.

Ya ce an baza jita-jita fiye da 21,000 cikin wata uku da suka gabata.

Akwai wani talla a wata tashar talabijin mai zaman kanta Extra News TV, wanda a ciki ake maganar wani labarin karya da ke cewa wai an gano gawarwakin yara su uku da aka cire ma sassan jikinsu a birnin Al Kahira.

Tallan ya kare da kira ga al'ummar kasar da su daina yarda da dukkan labarin da suka ci karo da shi a shafukan sada zumunta, kuma ya ce shafukan sada zumunta sun zama dandalin karya.

Sauran jaridu da kafofin watsa labarai ma na gudanar da wannan kamfen, kuma sun rika bayyana illar baza jita-jita, inda suke cewa labaran karya na iya durkusar da kasar.

Labaran karya sun zama takar ruwan dare, inda ake zargin ya taimaka wajen murda zaben da ya kai shugaban Amurka Donald Trump bisa mulki, kuma sauran kasashen Turai kamar Jamus da Burtaniya ma sun bayyana damuwarsu kan tasirin labaran kanzon kurege.