Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko fitar 'yan majalisun dokoki za ta kassara APC?
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Sauya shekar da wasu 'yan majalisar dattawa da majalisar wakilan Najeriya suka yi ya farfado da muhawarar da aka dade ana tafkawa a kasar, kan irin rabuwar kawunan da ake samu a jam'iyya mai mulki ta APC, da kuma irin 'mummunar' illar da hakan zai iya yi wa jam'iyyar.
A ranar Talata ne a wani al'amari mai kama da almara, 'yan majalisar dattawa 15 da kuma na wakilai 38 suka sanar da ficewarsu daga APC, inda mafi yawa suka sanar da komawarsu babbar jam'iyyar adawa ta PDP, wasu kuma ba su kai ga sanar da inda suka koma ba.
Dama dai an dade ana samun rarrabuwar kawuna a jam'iyyar ta APC musamman a jihohi, al'amarin da ya sa har wasu suka kauracewa babban taron jam'iyyar da aka yi a watan Yuni.
'Yan majalisun dai sun ce sun sauya sheka ne bayan da suka gama ganawa da masu ruwa da tsaki a mazabunsu.
Wani dan majalisar wakilai daga jihar Kano Sani Muhammad Rano, ya shaida wa BBC cewa sun sauya shekar ne saboda dalilai da dama.
"Yadda gwamnati ke tafiyar da al'amuranta bai yi mana dadi ba da kuma yadda ake tafiyar da shugabanninmu da jagororinmu, da halin da kasa take ciki, ana ta kashe-kashe da sace-sacen mutane.
"Kullum idan muka gabatar da batun a majalisa muka kawo mafita muka mikawa gwamnati ba ta komai a kai, sai dai kawai kullum mu dinga yi wa wadanda suka mutu addu'a.
"Don haka muka ga ba a kan haka muka zabi wannan gwamnati ba, mun zabe ta ne don kawo sauyi, kuma tun da ba mu samu sauyi ba, ya kamata mu sake sauya wannan sauyin," in ji Honorabul Rano.
Ana ganin wannan al'amari dai a matsayin wani abu da zai iya raunata matsayin Shugaba Muhammadu Buhari a majalisar dokoki, kuma hakan wata babbar barazana ce ga sake tsayawa takararsa a 2019.
Sai dai Farfesa Jibrin Ibrahim, masanin harkokin siyasa a Najeriya ya ce, abun bai zo masa da mamaki ba don da ma yawanci suna da matsala da jam'iyyar ko da shugaban kasa, "kuma da yawan su sun san jam'iyyar ba za ta tsayar da su ba."
"Babban abun mamakin shi ne yadda aka shafe tsawon shekara daya ana wannan tataburzar, amma sai a wannan makon ne shugaban kasa da na jam'iyya suka shiga tsakani don ba su hakuri.
Latsa hoton da ke sama don sauraron sharhin Farfesa Jibrin ibrahim:
PDP ta yi maraba da masu sauya shekar
Tuni dai jam'iyyar PDP ta yi maraba da sabbin 'ya'yan da ta samu sakamakon sauyin shekar da suka yi.
Mai magana da yawun PDP Kola Ologbondiyan ya shaida wa BBC cewa suna maraba da bakin nasu. "Wannan wani babban ci gaba ne ga a tafarkin demokuradiyyar Najeriya," a cewarsa.
Ya kara da cewa hakan zai ba su damar tserar da kasar daga manufofin "kama-karya na Shugaba Muhammadu Buhari" da kuma bai wa jama'ar kasar mulki mai inganci.
Martanin APC
Sai dai a nasa bangaren, shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya ce ya yi murna da sauya shekar da 'yan majalisun jam'iyyar suka yi.
Mr Oshiomhole ya shaida wa manema labarai bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari cewa wadanda suka fita din sojojin haya ne.
Ya kara da cewa hankalin jam'iyyar bai tashi ba ko kadan, kuma hakan ba zai shafi nasararta a zabukan 2019 ba.
Jam'iyyar ta kuma umarci 'ya'yanta da su kwantar da hankalinsu, inda ta ce har yanzu suke da mafi rinjaye.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da batun, inda ya ce yana yi wa 'yan majalisar fatan alheri. Kuma ya bukaci sauran 'yan jam'iyyar kada su karaya bayan faruwar hakan.
Ya ce jam'iyyar ta yi kokarin hana masu sauya shekar, "kuma wajibi ne na yaba wa kokarin shugabancin jam'iyyar game da yadda ya rika aiki ba dare, ba rana don hada kan jam'iyyar da kuma daidaita al'amarin don samun nasara a nan gaba," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Wa ya fi rinjaye a majalisa?
Batun jam'iyyar da ta fi rinjaye a majalisun dai wani abu ne da ake ganin shi ne ma fi muhimmanci a wannan al'amari.
A yanzu dai 'yar manuniya ta nuna cewa jam'iyyar PDP ce ke da mafi rinjaye a majalisar dattawan kasar inda ta fi APC da mutum 10.
Sai dai har yanzu babu tabbas kan bangaren da ya fi rinjaye a majalisar wakilan.
Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce a yanzu 'yar manuniya ta nuna cewa APC ba ta da rinjaye a majalisa, "kuma hakan zai iya jawo mata matsala sosai, don kafin nan da zabe za su iya yin abubuwa da dama da za su lalata irin ayyukan da gwamnati ke son gabatarwa.
Wanne tasiri sauyin shekar zai yi?
Idayat Hassan, Darakta ce a Cibiyar Demukradiyya da Ci-gaba (CDD), kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa, ta ce a yanzu PDP ta kara samun tagomashi a majalisar dokokin kasar.
"Dama can jam'iyya mai mulki na fuskantar tarnaki wajen gabatar da sabbin dokoki: alal misali ana daukar lokaci kafin a fitar da kasafin kudi.
"Wannan abu da ya faru na nufin APC tana cikin tsananin rikici saboda a yanzu zai yi wa mutane wahala su hade waje daya.
"Sannan abubuwa kamar girke 'yan sanda a kofar gidajen shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa abu ne da ka iya batawa gwamnati suna, saboda ya yi kama da bi-ta-da-kullin siyasa.A ganin Idayat Hassan, a yanzu tsige shugaban kasa abu ne mai yiwuwa, "Matakai ne masu sarkakiya, kuma da wuya hakan ta faru cikin wata shida kafin babban zabe, amma 'yan adawa za su iya taso da maganar don aika wani sako," in ji ta.
Shi ma Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce a yanzu ba za a iya sanin tasirin sauyin shekar ba, dalili shi ne a APC an san Buhari ne zai yi takara amma ba a san dan takarar PDP.
"Sai an san waye dan takarar PDP sannan za a san ko zai iya takara da Buhari ko ba zai iya ba."
Rashin cikakkiyar doka
Akwai muhimmiyar tambaya a kan ko idan mutum ya sauya sheka yana da ikon ci gaba da rike mukaminsa.Idayat ta kara da cewa: "Wani abin dubawa kuma shi ne cewa har yanzu ba a gwada tasirin dokar sauya sheka ba.
"A Najeriya mutane na zabar jam'iyya ne ba wai cancantar mutum ba, don haka sauya jam'iyya na dasa ayar tambaya kan matsayin kujerar mutumin da ya sauya sheka.
Ba wannan ne karo na farko da irin wannan sauyin shekar ya faru a Najeriya ba, ko a shekarar 2014 ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wasu gwamnoni biyar sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Kuma mafi yawan mutanen da suka sauya sheka a yanzu, su ne dai wadanda suka koma APC daga PDP a wancan lokacin.