Me ke tsakanin shugaban Faransa da shugabar Croatia?

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya na ta yin tsokaci kan ko wanne dalili ne ya sa Shugabar kasar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović ta dinga kasancewa kusa da Shugaban faransa Emmaneul Macron, a yayin wasan karshe na gasar cin kofin duniya, duk kuwa da cewa matar Mista Macron na wajen.

Wasu da dama sun yi ta wallafa hotunan Mista Macron tare da Kolinda Grabar-Kitarović, inda a wurare da dama aka nuna su ko dai suna rungume da juna ko kuma suna sumbatar juna.

Hakan ya sa wasu ma'abota shafukan sada zumunta suka dinga zargin cewa ko dai da wani abu a tsakanin shugabannin biyu ne, yayin da wasu kuma suka dinga jajantawa matar shugaban kasar Faransan.

Shi ma dai mijin shugabar ta Croatia ya halarci wasan. Kawo yanzu babu wani martani daga shugabannin biyu ko kuma gwamnatocinsu.

Faransa ce ta doke Croatia da ci 4-2 inda ta lashe gasar, wacce aka fafata a kasar Rasha.

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

@parislima ya rubuta cewa: "Emmanuel Macron ya yi shugabar kasar Croatia wata kyakkyawar sumbata yayin da matarsa Brigitte Macron ke ta faman rawa."

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi ma wani mai shafi @nahdhi89 ya rubuta cewa: "Ba zan maki fatan komai ba sai na alkhairi Brigitte Macron."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

"Ina taya Faransa murnar samun nasara amma gaskiya na ga Brigitte Macron ba ta cikin farin ciki ...@ Ga Emmanuel Macron da shugabar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović," a cewar @SeidGoro.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wannan sakon na sama kuwa cewa yake: "Me yake faruwa ne da shugaban Faransa da takwararsa ta Croatia? Sai taba juna da sumbatar juna suke yi."

A farkon fara wasan dai Shugaba Macron da Shugabar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović da na Rasha Vladimir Putin da shugaban hukumar FIFA da Sarkin Qatar na zaune ne daga gaba-gaba, waje na musamman da aka ware musu.

Amma daga bisani sai Sarkin Qatar Tameem bin Hammad Al Thani ya tashi ya nemi matar Mista Macron da ta koma wajensa kusa da mijinta ta zauna, shi kuma ya koma bayansu inda take zaune.

Wasu ma'abota shafukan sada zumuntar dai sun yi ta wadannan kalamai ne suna mai alakanta sabuwar alakar da aka gani tsakanin Mista Macron da shugabar Croatia da yawan shekarun matarsa Brigitte Macron mai shekara 65, yayin da shi kuma yake da 45.

Ita kuwa shugabar Croatia tana da shekara 50 ne kuma ita ma tare da mijinta ta je kallon kwallon amma ba a nuna ta kusa da shi ba, kuma ba a gansu tare a hotuna ba sosai kamar yadda aka yi ta ganinta da shugaban Faransa.

Sai dai ga dukkan alamu tsananin farin ciki da nishadin da shugabannin biyu ke ciki ne ya sa suka dinga kasancewa da juna, tare da runguma ko sumbatar juna a duk lokacin da bangare daya ya zura kwallo.

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images

Macron da shugabar Croatia

Asalin hoton, Getty Images