Kotun koli ta wanke Bukola Saraki

Asalin hoton, Facebook/Nigerian Senate
Kotun Kolin Najeriya ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.
A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta shigar da karan Saraki kan tuhume-tuhume 18 na yin karya wajen bayyana abin da ya mallaka.
Duka alkalan kotun kolin biyar sun amince da wannan hukuncin, inda suka yi watsi da sauran tuhume-tuhume uku kuma suka ce hujjojin da lauyoyin gwamnati suka gabatar raunana ne.
Sanata Saraki ya yi maraba da hukuncin, yana mai cewa dama siyasa ce kawai ta sa gwamnati shigar da karar tun farko.
Ya ce an kai shi kotun ne domin "cimma bukatar wasu mutane wadanda ba su ji dadin zamowarsa shugaban majalisar dattawa ba".
Wata sanarwa da Bukola Saraki ya sanya wa hannu da kansa, ta ce shugaban majalisar ya gode wa Allah (Madaukakin Sarki) kan nasarar da ya samu, wacce ta wanke shi baki daya kan batun.

Asalin hoton, Getty Images
Ya kara da cewa hukuncin ya tabbatar da imanin da ya ke da shi kan tsarin shari'ar kasar, sannan ya godewa Sanatoci da 'yan majalisar da suka rinka mara masa baya a lokacin shari'ar.
Masu sharhi na ganin wannan ba karamar nasara ba ce ga Saraki, wanda batun shari'ar ya mamaye mulkinsa na majalisar ta dattawa a shekara ukun da ta gabata.
Yadda shari'ar ta gudana
A watan Yunin bara ne Alkalin kotun da'ar ma'aikata Danladi Umar ya fara yin watsi da tuhume-tuhume 18 da ake wa Saraki.
Daga nan ne sai Ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a daukaka kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja.
Sai dai a hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a watan Disambar bara, ya dawo da tuhume-tuhume uku cikin 18 da ake masa kuma ya umarce shi da ya koma kotun da'ar ma'aikata don ya sake kare kansa.
Daga nan ne sai Saraki ya daukaka kara zuwa kotun kolin, inda yake kalubalantar hukuncin kotun daukaka karar na dawo da tuhume-tuhume ukun.










