Shin me ya sa wasu ba su damu da gasar kofin duniya ba?

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da gudanar da gasar cin kofin duniya ta bana a kasar Rasha, inda hankalin magoya bayan kwallon kafa da sauran jama'a ya karkata kan gasar.
Sai dai duk da cewa gasa ce da ke jan hankalin jama'a a sassan duniya daban daban, akwai wasu da ba su damu da wasan ba.
Shin ko me yasa haka?
BBC ta yi nazari kan dalilin da ya wasu ba sa sha'awar gasar da kuma irin abubuwan da su ke mayar da hankali a kai.








