Zuwa na taron APC zai iya haifar da abin kunya – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zuwansa taron APC a Abuja zai iya haifar da abin kunya da rikici a jam'iyyar.

A sanarwar da ya fitar, Kwankwaso ya bayyana dalilan da suka sa ya kauracewa babban taron na APC da aka gudanar a Abuja domin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar na kasa.

Kwankwaso wanda bangarensa ya gudanar da nashi zaben shugabannin jam'iyyar a matakin mazabu da kananan hukumomi da jiha ya ce ya kauracewa taron ne saboda yadda jam'iyyar ta ki amincewa da zaben da suka gudanar.

"Ina ganin gabatar da kanmu a irin wannan muhimmin taro ba zai kasance bukatun dukkanin taron ba idan ma an amince mu taka kafarmu a taron" in ji Kwankwaso.

Ya kara da cewa zuwansa na iya haifar da abin kunya da rikici fiye da wanda aka gani a runfar wakilan jihar Imo da Delta a ranar Asabar da aka soma taron.

Sai dai kuma duk da ya kauracewa taron, amma a cikin sanarwar da ya fitar, tsohon gwamnan na Kano ya taya Adams Oshiomhole murna kan nasarar zabensa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC.

Sannan ya yi wa sabbin shugabannin jam'iyyar fatan alheri ga shirin da za su fara na hada kan 'ya'yan jam'iyyar APC.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin 'yan sabuwar PDP da ke zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sai dai kuma akwai wasu daga cikin `yan sabuwar PDPn da suka halarci taron na APC, ciki har da shugaban majalisar dattawa Senata Bukola Saraki, da Kakakin majalisar wakilai Hon. Yakubu Dogara.

Duk da cewa har yanzu bai fito ya bayyana aniyar tsayawa takarar zaben shugaban kasa ba, amma 'yan Kwankwasiya na ci gaba da tallar tsohon gwamnan na Kano.

Magance rikicin APC zai kasance babban kalubalen Adams Oshiomhole sabon shugaban jam'iyyar na kasa da aka zaba.