Ingila ta kai zagaye na biyu, Japan ta rike Senegal

Ingila ta caccasa Panama 6-1 a rukuninsu na G, wanda ya ba ta damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Ingila ta samu maki shida a wasanni biyu da ta buga kafin ta hadu da Belgium a wasan karshe a rukuninsu da ya kunshi Tunisia da kuma Panama.
Kwallaye uku kaftin din Ingila Harry Kane ya ci shi kadai, inda yanzu ya sha gaban Ronaldo a matsayin wanda ya fi yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya a Rasha.
John Stones ya ci wa Ingila kwallaye biyu yayin da Jesse Lingard ci kwallo daya.
Yanzu Ingila ce saman Belgium a teburin rukuninsu saboda ba ta da katin gargadi da yawa.
Senegal da Japan sun rike juna
Japan da Senegal sun raba maki ne tsakaninsu bayan sun rike juna 2-2.
Senegal ce ke fara cin kwallo a raga kafin daga baya Japan ta farke.
Wasan ya haramtawa Senegal zama kasa ta farko daga Afirka da ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar da ake gudanarwa a Rasha.
Haka ma sakamakon ya haramtawa Japan tsallakewa zuwa zagaye na biyu, a matsayin kasa ta farko daga yankin Asiya da ta tsallake a gasar.

Senegal wacce ta doke Poland a wasan farko a rukuninsu na H za ta fafata ne da Colombia a ranar 28 ga wata.
Japan kuma za ta kara ne da Poland duka wasannin a lokaci daya.











