World Cup 2018: 'Yadda na je Rasha a keke don na ga Messi'

Clifin Francis riding his bike

Asalin hoton, Clifin Francis

    • Marubuci, Daga Vikas Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi

Clifin Francis ya kasance yana zaune ne a gida a kudancin Indiya a lokacin da wani abokinsa ya tambaye shi kan ko zai je gasar kofin duniya ta kwallon kafa.

"Kwarai kuwa," in ji shi. "Zan iya zuwa Rasha domin ganin kasaitaccen bikin."

An yi wannan maganar ce a cikin watan Agusta - amma bai san yadda zai sami kudin tikitin jirgi daga inda yake zama a garin Kerala ba. Mista Francis wani malamin lissafi ne mai zaman kansa kuma yana samun dala 40 (kimanin naira 14,400) a ko wacce rana.

"Na fahimci cewar ba zan iya samun isasshen kudin da zai kai ni Rasha in kuma yi zaman wata daya a can ba. Sannan na tambayi kai na - wacce hanyar tafiya ce za ta iya kasance wa wadda ta fi sauki? Hanyar keke ce amsar."

Abokanansa ba su yarda da shi ba, amma zuwa wancan lokacin ya riga ya yanke shawara.

Ranar 23 ga watan Fabrairu, ya fara wata tafiya mai cike da ban mamaki inda ya tafi Dubai ta jirgin sama, ya hau kwale-kwale zuwa Iran. Amma daga nan zuwa babban birnin kasar Rasha tazarar ta dara kilomita 4,200km (2,600 miles) inda yake son zuwa a keke.

Abin da ya ke nema a karshe, shi ne - damar samun ganin gwaninsa, Lionel Messi na Ajantina, wanda wasu ke yi wa kallon dan wasan da ya fi iya taka leda a duniya.

Clifin Francis riding his bike

Asalin hoton, Clifin Francis

Mista Francis ya shaida wa BBC cewar: "Ina son tuka keke kuma ina matukar kaunar kwallon kafa. Kawai sai na hada abubuwa biyu da na ke so."

Ya so ya yi tafiya ta Pakistan, amman dole ya sake shawara saboda yadda dangantaka ta yi tsami tsakaninta da Indiya.

'Kwallon kafa da fina-finai'

"Sauya shiri ya sa na yi rashi sosai. Ban iya na kai keke na Dubai ba saboda haka dan dole na sayi wani wanda ya kai dala 700 (kimanin naira 254,000). Ba wanda ya fi dacewa ga tafiya mai nisa ba, amma wannan shi ne abin da nake da karfin saya kenan," in ji shi.

Amma ya manta wannan koma-bayan lokacin ya shiga filin jirgin ruwan Bandar Abbas na kasar Iran ranar 11 ga watan Maris.

"Kasa ce wadda ta fi kyau a duniya, kuma mutanen suna karbar baki hannu bibiyu. Na shafe kwana 45 a cikin kasar, amma kwana biyu kawai na yi a otel," in ji shi.

Mista Francis ya yi tanadin kashe dala 10 ne a ko wacce rana, amma ya ce a duk inda ya je a Iran, mutane suna gayyatarsa ya zauna a gidajensu kuma suna yi masa tayin abijnci.

Clifin Francis with people during his travels

Asalin hoton, Clifin Francis

Clifin Francis' bike on a road between Iran and Azerbaijan

Asalin hoton, Clifin Francis

"Tunani na game da Iran ya sauya. Na fahimci cewa bai kamata mutum ya gina ra'ayinsa game da wata kasa ba bisa siyasar yanki," in ji shi.

Ya tuna gine-ginen kasar masu ban mamaki.

Ya ce: "wuyar tuka keke ta ragu sosai saboda kauyukan Iran masu kyau. Zan sake komawa.

"Sun sa na yi alkawarin cewar zan mara wa tawagar Iran baya idan na isa Rasha. Su ma suna kaunar Bollywood kuma wannan ya ba ni damar mutane su saki jiki da ni a wurare da dama," in ji shi.

"Gaskiya ce cewar kwallon kafa da fina-finai suna hada kan duniya."

Tuka keke ya sa ya rame

Daga nan sai ya tafi kasar Azerbaijan, inda jami'an shige da fice suka samu matsala wajen tantance takardun tafiyarsa - saboda ya rame sosai wurin tuka keke".

"Ban yi kama da hotonan da ke cikin fasfo di na ba. Jami'an tsaron sun shafe fiye da sa'o'i takwas wajen tantance bayanaina, amma sun taimaka mini."

Clifin Francis posing for a selfie

Asalin hoton, Clifin Francis

Mista Francis bai iya biyan kudin otel ba a Azerbaijan kuma a yawancin lokuta ya kafa tentinsa a kebabbun wurare ne.

"Mutane anan ma sun kasance kasance masu kyawawan halaye, amma sukan daukar lokaci kafin su saki jiki da bako. Na samu wasu Indiyawa da ke zama a babban birnin kasar Baku kuma na zauna da su zuwa wani lokaci."

Makalewa a 'garin da ba na kowa ba'

A lokacin da Mista Francis ya kai Georgia, an hana shi shiga, kuma ya zama dole ya sake sauya shirinsa, a lokacin da ya kusan zuwa birnin Moscow.

"Ina rike da dukannin takardu, amma ban san me ya sa aka hana ni shiga ba. Wannan ya saka ni cikin wani yanayi na rashin tabbas saboda izini (bisa) na shiga Azerbaijan na lokaci daya ne," in ji shi.

Mista Francis ya makale a garin da ba na kowa ba a tsakiyar Georgia da Azerbaijan cikin yini daya. Daga baya an ba shi bisar sake shiga Azerbaijan ta gaggawa.

Ya ce: "Sannan na sake neman wata hanya ta shiga Rasha. Wani ya shaida mini cewa Azerbaijan tana da bakin iyaka da yankin Dagestan na kasar Rasha.".

"Na je wannan wurin ba tare da sanin cewa wuri ne da ake ganin yana cike da rashin tsaro ba. Amma ba ni da zabin komawa baya, kuma na shiga Dagestan ranar biyar ga watan Yuni."

Clifin Francis with people during his travels

Asalin hoton, Clifin Francis

Ya kara da cewa harshe ya kasance wata babbbar matsala saboda da wuya a samu wadanda suka iya Turancin Ingilishi a Dagestan.

"Mutane sun yi mamakin ganin ba-Indiye ya shiga yankinsu kan keke. Na sake amfani da harshen kwallon kafa da na fim wajen saka mutane su saki jiki da ni."

A halin yanzu Mista Francis ya na dab da birnin Moscow. Yana bukatar kasancewa a babban birnin kasar zuwa ranar 26 ga watan Yuni domin kallon fafatawa tsakanin Faransa da Denmark.

"Wasan da na samu na sayi tikicin shiga kenan," in ji shi.

Argentina vs Iceland - Spartak Stadium, Moscow, Russia - June 16, 2018 Argentina"s Lionel Messi misses a penalty

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Lionel Messi ya kware sosai - amma zai so ya mance da fenaretin da ya barar a wasansu da Iceland

"Amma ina goyon bayan Argentina kuma Lionel Messi ne na fi so - Ina bauta masa. Ina fatan haduwa da shi in kuma neme shi ya rattaba hannu kan keke na."

Clifin Francis na fatan cewa tafiyarsa zai bai wa mutane karfin gwiwa game da kwallon kafa da kuma motsa jiki domin tabbatar da lafiyar jiki.

"Ina fatan ganin Indiya za ta samu shiga gasar kofin duniya wata rana. Kuma wannan zai faru ne kawai idan an samu karin yara da suke wasan kwallon kafa a Indiya. Ina da kwarin gwiwa game da damarmakinmu cikin shekara 20 masu zuwa," in ji shi.

"Ina fatan cewa mutane za su soma hawan keke bayan sun karanta labari na.

Clifin Francis with people during his travels

Asalin hoton, Clifin Francis

"Hawan keke yakan mayar da mutun yadda ake a da can. Abin da kake bukata daga baya shi ne wanka, inda za ka saka tenti da kuma abinci mai kyau, za ka yi farin ciki.

"Zan yi murna idan tafiyata ta sa wani yaro ya fara buga kwallon kafa a Indiya."