Fazlullah: An kashe shugaban Taliban a Afghanistan

Mullah Faizullah

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban kungiyar Taliban reshen Pakistan Mullah Faizullah

Rahotanni daga Afghanistan na cewa an kashe shugaban kungiyar Taliban ta Pakistan a wani harin da Amurka ta kai da jirgin sama mai sarrafa kansa.

Ana tuhumar Mullah Faizullah da hannu kan harin da aka kai wa Malala Yusufzai da wasu hare-hare kan manyan mutane a Pakistan.

Kakakin ma'aikatar tsaron Afghanistan ya fada ma BBC cewa an kashe Faizullah ne a yankin Kunar a kusa da iyakar kasar da Pakistan.

Fazlullah yayi kaurin suna, inda har ake masa kirari da sunan Rediyon Mullah, saboda salon wa'azinsa da yake watsawa ta wata tashar rediyo a yankin Swat Valley na Pakistan.

Ya zama Amirun kungiyar Taliban reshen Pakistan a 2013, kuma a karkashin mulkinsa ne kungiyar ta kai wani mummunar hari akan wata makaranta a birnin Peshawar.

Harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 150, yawancinsu yara kanana, kuma tun bayan wannan harin ikon kungiyar yayi ta raguwa.

Dakarun Pakistan sun yi nasarar fatattakar kungiyar, dalilin da yasa sauran 'ya'yanta suka tsere zuwa makwabciyar kasar Afghanistan ta kan iyakokin kasar, amma sun cigaba da kai hare-hare zuwa cikin Pakistan.