Donald Trump da Kim Jong-un sun isa Singapore inda za su tattauna

Bayanan bidiyo, Yadda Kim Jong-un ya isa Singapore

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un sun isa Singapore domin tattaunawar da za su yi mai cike da tarihi.

Mista Trump ya isa, sa'o'i bayan Mista Kim da tawagarsa sun isa Singapore.

Haduwarsu, ita ce ta farko tsakanin shugaban Koriya ta Arewa da shugaban Amurka.

A ranar Talata ne shugabannin biyu za su yi ganawar da duniya ta dade yana jira a tsibirin Sentosa na Singapore.

Trump ya bayyana ganawar a matsayin "wani abu na lokaci daya" a zaman lafiya tare da cewa su biyu sun kasance a kasar da ba su sani ba.

Amurka na fatar tattaunawar za ta bude kofa ga tsarin da zai sa Kim Jong-un ya hakura da makaman nukiliya.

Shugabannin biyu sun dauki lokaci suna yi wa juna barazana tare da musayar zafafan kalamu kafin amincewa su hadu gaba da gaba.

Kim Jong-un a Singapore

Asalin hoton, Singapore/MOCI

Bayanan hoto, Kim Jong-un ya riga Shugaban Amurka Donald Trump isa Singapore

Mista Kim ya gana da Firaministan Singapore Lee Hsien Loong bayan ya isa.

Ana sa ran Mista Trump zai gana da Firaministan na Singapore kafin soma tattaunawarsu da Mista Kim.

Donald Trump a Singapore

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Donald Trump iso Singapore daga taron G7 a Canada

A watan Maris ne Donald Trump ya amince ya yi ganawar keke da keke da Kim Jong-un.

Amma tun daga wannan lokacin, aka shiga rashin tabbas ga tattaunawar, inda Mista Trump ya taba fitowa yana cewa ba za a yi tattaunawar ba, amma bayan bin hanyoyi na diflomasiya, yanzu shugabannin biyu za su zauna su tattauna.

Singapore ita ce kasa ta uku da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya taba ziyarta tun zamansa shugaban kasa a 2011.

Ya taba zuwa China a watan Maris, ziyararsa ta farko a matsayin shugaban Koriya ta Arewa a wata kasa.

A watan Afrilu, Kim Jong-un ya kasance shugaban Koriya ta Arewa na farko da ya taka kafarsa zuwa Koriya ta Kudu inda ya gana da shugaban kasar Moon Jae-in.