'Yan bindiga sun sace matan wani dan kasuwa a Birnin Gwari'

Wasu 'yan Bindiga da ba a tantance ba sun yi garkuwa da matan wani dan kasuwa su guda uku a karamar hukumar Birnin Gwari da ke cikin jihar Kaduna.
'Yan bindigar sun kai harin ne a garin Maganda cikin dare kafin wayewar safiyar Lahadi suka sace matan Alhaji Ado Nakwana guda uku.
Wani mazauni Maganda makusanci ga dan kasuwar ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun shiga kauyen kusan karfe biyu na dare, kuma kai tsaye suka isa gidan dan kasuwar suka bude wuta a kofar gidansa.
Ya ce sun tafi da matansa guda uku bayan ba su iske shi ba ya gudu a lokacin da suka shiga gidan.
"Amma daga baya sun sako daya daga cikin matan tare da ba ta sakon numbar waya ta kawo wa mijinta", a cewarsa.
Ya kuma ce sun harbi wani matashi makwabcin dan kasuwar, bayan ya bude daki ya fito a lokacin da suka kai harin. Ya ce an tafi da shi asibiti a Kaduna.
Uwar gidan dan kasuwar da wadda ke bi ma ta ne yanzu ke hannun 'yan bindigar bayan sun sako ta uku.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin 'yan sanda amma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ASP Aliyu Mukhtar bai dauki waya ba.
Wannan na zuwa a yayin da wasu rahotanni suka ce 'yan bindiga sun kaddamar da hari a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda suka sace wani direba kafin daga bisani ya tsere daga hannunsu.
Yankin Birnin Gwari a Kaduna na cikin yankunan arewa maso yammaci da ake yawan samun matsalar sace-sacen mutane domin kudin fansa.











