Yadda Akuyar Najeriya ta zama abar kallo a Amurka

Mutanen Amurka sun shaku da Akuyar Najeriya kamar sauran dabbobin gida irinsu Kare da Mage.

Dalibai na gudanar da wasannin motsa jiki tare da Akuyar ta Najeriya a wuraren da aka ware domin motsa jiki.

Wasannin motsa jiki tare da Akuyar ta Najeriya yanzu abu ne da ake gudanarwa a sassan Amurka.

Bayanai sun ce tun a 1950 aka tafi da gajerun Awakin zuwa Amurka wadanda mafi yawanci aka fi samu a kudancin Najeriya.

Ana amfani da Akuyar wajen samar da madara da kuma wasanni a gida saboda kankantarta.

Ga wasu hotunan yadda ake wasannin motsa jiki da gajerun Awakin a biranen Los Angeles da Califonia na Amurka.