Da gaske ne matasan Najeriya na zaman kashe wando?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Stephanie Hegarty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Lagos
Kalaman da shugaban Najeriya ya yi na cewa, yawancin matasan kasarsa malalata ne, ba abune da ya dace ya yi a yayin wani taro na kasashen waje ba.
Wannan shi ne abinda wasu 'yan kasar ke ganin sam bai dace Shugaba Muhammadu Buhari ya furta hakan ba a yayin ziyarar da ya kai London a akwanakin baya.
Da ya ke jawabi a yayin taron kungiyar Commonwealth da ya gudana kwanan nan, Shugaba Buhari ya ce, "Da yawa daga cikin matasan kasarsa, suna zaman banza ba tare da aikin komai ba, amma suna jiran gwamnati ta samar musu gida da inshorar lafiya da kuma ilimi kyauta".
Wani abin mamakin shi ne, sai kawai aka rinka wallafa kalaman a kafofin sada zumunta inda ake sanya maudu'in #LazyNigerianYouths.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a baya-bayan nan, shugaban ya kare kalaman da ya yi. Mataimakinsa a bangaren yada labaran ya yi nuni da cewa, shugaban sam bai yi amfani da kalmar "malalata ba".
Wani sakon Twitter da wani ya wallafa ya ce "Ni na kammala karatu na da digiri mai daraja ta biyu a bangaren hada sinadarai wato Chemistry a jami'ar Lagos, abin mamakin shi ne yanzu ni mai hada takalmi ne saboda ban samu aiki ba. Don haka ni ba malalaci ba ne".

Asalin hoton, AFP
Domin gano zahirin irin ce-ce-ku-cen da wannan kalamai suka janyo, BBC ta yi nazari, sannan kuma ta yi tambayoyi a kasar da ta yi suna wajen buga-buga, matasan kasar nawa ne su ke taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar?
Idan ka tambayi 'yan Najeriya me suke yi domin ciyar da rayuwarsu gaba, a kalla za ka samu amsoshi biyu ne kawai daga garesu, wasunsu su ce ba komai, wasu kuwa suna da abin yi.
Yayin da shugaban kasar a cikin kalamansa ya ce, kaso 60 cikin 100 na al'ummar kasar matasa ne 'yan kasa da shekara 30, hakan ya kai yawansu miliyan 107.
Mafi yawansu kuma shekarunsu ya kai ace suna aiki, amma kuma ba su samu aikin ba.
Matsalar rashin aikin yi a Najeriya, ta rubanya har sau uku tun daga shekarun 2014 zuwa 2017 inda ta kai daga kaso 6.4 cikin 100 zuwa kaso 18 cikin 100, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.
Matsalar ta karu tsakanin 'yan shekara 15-34, kamar yadda ta karu a tsakanin masu shekaru da yawa.
To amma an samu bambanci sosai daga tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017, inda matsalar tsoffin ma'aikata ta karu da kaso 3.9, yayin da a bangaren matasa kuma aka samu karuwar matsalar rashin aikinyin da fiye da miliyan takwas.
A gefe guda kuma, tattalin arzkin Najeriya, wanda ya dogara a kan danyen man fetur din da kasar ke fitarwa, ya durkushe sakamakon faduwar farashi a kasuwannin duniya. Don haka ba abin mamaki ba ne idan galibin wadannan matasa suka yi ta fadi-tashin neman aiki — kuma hakan ne ya faru.
Ko da yake kasar ta fuskanci koma-bayan tattalin arziki, a tsakanin (matasa da manya) yawan mutanen da suka samu aiki ya karu da kusan miliyan daya. (Najeriya ta farfado daga durkushewar tattalin arziki ne a watan Satumban 2017)
Saboda haka duk da rashin kwarewarsu, matasa da yawansu ya kai gwargwadon yawan manyan da basu rasa aikinsu ba ko ma suka samu sabbin ayyukan yi.
Yana da matukar muhimmanci mu duba mutanen da ba a biyansu wani kudin kiriki, misali wadanda suke aikin sa'a 40 a mako, inda albashinsu bai dace da matsayin karatunsu ba.
Kaso 40 cikin 100 na al'ummar Najeriya wanda ya kai mutum miliyan 80, ba su da aikin yi ko kuma suna aikin da albashin bai taka kara ya karya ba.

Asalin hoton, AFP











