Yadda Kodin ke haukatar da matasa a Najeriya

Lokacin da kanin wakiliyar BBC Ruona Meyer ya zama dan Kodin, sai ta fara bincike kan mutanen da ke hadawa da kuma sayar da wannan maganin tari a kan titunan birnin Legas.

Binciken ya kai ta har cikin manya-manyan masu aikata laifuka a Najeriya, inda ta gano wani lamari ko bala'ai da ke rusa rayuwar matasa a Afirka ta Yamma.

"A inda ake da yara 'yan makaranta, da zarar sun dandana, sai su ci gaba da matsawa sain an kara musu," a cewar Junaid Hassan.

Lokacin da na ji ya fadi haka sai na ji ciki na ya kama ciwo.

Tuni na riga na ga abin da ya ke magana a kai, matasan Najeriya da suke buguwa saboda shan wannan kwayar wacce ke sa mutum ya shaku da ita.

Daga matashiyar yarinya a Legas wacce iyayenta suka rasa yadda za su taimaka mata. Da kuma wani matashi a Kano, da aka daure da sarka a wata cibiyar kula da masu shaye-shaye, inda kudaje ke binsa saboda ya haukace sakamakon shafe watanni yana shan Kodin tare da abokanansa.

Dan uwana ya yi fama da bala'in shan Kodin bayan mutuwar mahainfinmu. Maganin mai kamshin itacen nan na Strawberry kan sa mutum ya bugu kuma ya ji baya iya rabuwa da shi.

Masu hadawa da sayarwa na bi lungu-lungu da kuma gidajen shakatawa cikin dare domin sayarwa. Matasa kan hada shi da lemun kwalba ko kuma su sha shi kai tsaye daga kwalbarsa a wuraren da ake "biki ko gasar shansa".

Mr Hassan, wanda ake kira Baba Ibeji, yana aiki a kamfanin hada magunguna na Bioraj Pharmaceuticals, wanda ke da izinin hada maganin tari da ake kira Biolin. Kamfanin na sahun gaba wurin kai magani arewacin Najeriya.

Yana daga cikin ma'aikatan kamfanonin magani da BBC ta nada cikin sirri, inda suke sayar da Kodin ba bisa ka'ida ba a 'yan watannin suka gabata. Ya halatta a hada ko sayar da maganin, amma kuma haramun ne a sayarwa da mutum ba tare da nuna shaidar cewa likita ne ya ba shi/ta izinin sha ba.

"Idan mutum yana son katan 1,000, za mu sayar ba tare resiti ba," a cewar Mr Hassan, wanda ke bayanin yadda suke kaucewa doka, duk da cewa hakan ya sabawa ka'idojin kamfanin Bioraj.

Lokacin da muka sanar da Bioraj cewa muna da shaidar da ke nuna cewa Mr Hassan na sayar da maganin ba bisa ka'ida ba, sai suka ce su ba sa sayarwa ba bisa ka'ida ba, kuma shugaban kamfanin Bioku Rahamon ne ke kula da cinikin Biolin.

Maganin Kodin - yadda girman matsalar ta ke

  • Kodin magani ne da ke rage zafin ciwo ko na jiki amma yana cikin magungunan da ke sa maye.
  • Idan aka sha shi fiye da kima, to yana janyo tabin hankali kuma yana yin illa ga koda ko hanta ko zuciyar mutum
  • An fi hada maganin tari na kodin da lemun kwalba kuma dalibai ne suka fi shansa.
  • Daga kasashen waje ne ake shigowa da kodin, amma a cikin Najeriya ne kamfanoni fiye da 20 suke hada magani
  • Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar na kokarin kawarda da matsalar.
  • A samamen da taka kai a baya-baya nan, ta kwato kwalaben Kodin 24,000 daga cikin wata babbar mota a jihar Katsina.
  • Ta'ammali da kodin babbar matsala ce a Afirka, inda ake samun rahotanni game da wadanda ba su iya rabuwa da shi a Kenya da Ghana da Niger da kuma Chadi
  • A shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta hana amfani da shi a kasar sakamakon rahoton da ta samu game da yawan masu ta'ammali da shi a matsayin kayan maye

Kamfanoni da masana harkar magunguna da ke wannan harka suna sane da irin illar da ya ke haifarwa.

Daga cikinsu akwai Chukwunonye Madubuike, babban jami'in kasuwanci a Emzor pharmaceuticals, wanda ya sayar mana da kwalba 60 ba bisa ka'ida ba a wani hotel a Legas.

Daga bisani Emzor Pharmaceuticals sun shaida mana cewa suna bincike kan lamarin, sannan suka ce ba shi da maganin da yawa da har zai iya sayarwa da yawa.

' Ya shafi kowa da kowa'

Hukumar kula da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Kano (NDLEA) ita ce ke kai samame domin kwace kodin a hannun matasa da kuma masu sayarwa ba bisa ka'ida ba.

Sun nuna mana tan biyu na kalar maganin kirar Bioraj wanda jami'anta suka kwace. Sun kuma nuna mana makaman da miyagu ke amfani da su domin kare wannan sana'a ta su ta hanyar kai wa jami'an NDLEA hari.

A cewar gwamnatin kasar a kullum kimanin kwalaben kodin miliyan uku ake shanye wa a jihohi biyu kadai da ke arewacin kasar - Kano da Jigawa.

Hukumar NDLEA ta ce ta na shan wuya wurin shawo kan lamarin.

A wata cibiyar lura da masu shaye-shaye da ke unguwar Dorayi a cikin birnin Kano, wasu daga cikin masu shaye-shayen na cikin mari don tsoron kada su far wa mutane.

Wata matashiya mai shekara 16 a duniya da ke cibiyar kula da masu shaye-shaye ta Dorayi, ta bayar da shawara ga sauran matasa.

"A gaskiya ina basu shawarar kada su shiga ta'ammali da shi, idan har basu fara ba, don yana lalata rayuwa" in ji matashiyar.

Amma yayin da wadannan mutane masu hadawa da sayar da kodin ba bisa ka'ida ba suke ci gaba da kasuwancinsu ba wata tsangwama ba, illar hakan na fadawa ne a kan matasan kasar a cikin wannan matsalar da ke kara kamari.

Wannan shi ne rahoto na farko na sabon sashin bincike na BBC Afrika da ake kira Africa eye.