Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wanda ya ci gasar cin attaruhu ya tsinci kansa a asibiti
Wani mutum wanda ya ci attaruhun da ya fi ko wanne yaji a duniya a wajen gasar cin barkono ya samu kansa a gadon asibiti bayan da ya hadu da wani gigitaccen ciwon kai mai kamar saukar aradu a ka.
Mutumin mai shekara 34 ya ci attaruhun ne safurin Carolina Reaper a wajen agasar da aka yi a birnin New York na Amurka.
Ya fara mummunan ciwon kan ne kwanaki kadan bayan cin attaruhun.
An bayyana lamarin ne a wani rahoto na BMJ Case Reports saboda shi ne al'amari na farko da aka samu dangane da cin attaruhu mai zafi.
Likitan da ya duba shi ya gargadi duk wanda ke cin attaruhu mai zafi da cewa ya je ya ga likita da gaggawa tun kafin ya hadu da matsanancin ciwon kai.
Ciwon kai mai kamar saukar aradu na afkuwa ne idan jijiyoyin da jini ke bi ta kwakwalwa suka takure.
Jim kadan bayan lashe gasar sai mutumin ya fara jin juwa.
Bayan kwanaki kadan sai ya fara ciwon wuya da kuma ciwon kai.
Daga baya sai ciwon ya tsananta inda har aka kwantar da shi a dakin gaggawa, aka kuma yi masa gwaje-gwajen da suka shafi kwakwalwa, amma ba a ga komai ba.
Amma wani hoton kwakwalwasa da aka dauka sun nuna yadda jijiyon kwakwalwar suka kumbura, inda likitoci suka ce ya hadu da cutar reversible cerebral vasoconstriction syndrome (RCSV).
Attaruhun da ya fi ko wanne yaji a duniya
- Attaruhun Carolina Reaper yana da tsananin yaji
- A shekarar 2013 ne kundin mutane da al'amura mafiya shahara na duniya Guinness World Records ya ayyana shi a matsayin mafi yaji
- Kamfanin Ed Currie from da Pucker Butt ne suka samar da shi a Kudancinh Carolina fiye da shekara 10
- Ya fara shuka attaruhu ne bayan da ya gano cewa akwai wani sinadari mai yaki da cutar kansa a cikin attaruhun
Za a iya cewa ba wani takaimaimai abu da ke jawo cutar RCVS, amma ta kan faru idan an sha wasu kwayoyin magani da ba su dace ba.
Wannan ne karo na farko da aka alakanta cutar da cin attaruhu. Amma a baya an taba alakanta cin wani nau'in borkono da ciwon zuciya.
Dr Kulothungan Gunasekaran, na Asibitin Henry Ford Hospital da ke Detroit, wanda ya rubuta rahoton, ya ce akwai bukatar mutane su dinga kula da haduran da ke tattare da cin borkono.