Kun san shugabannin Afirka da aka gurfanar a kotu?

Pasteur Bizimungu - tsohon shugaban kasar Rwanda

A shekarar 2004 ne aka daure Pasteur Bizimungu bisa samunsa da laifin kafa mayakan sa-kai da almubazzaranci da dukiyar kasa da kuma tunzura mutane su yi bore.

Sai dai mutane da dama na ganin an yi hakan ne domin cimma burin siyasa.

Frederick Chiluba - tsohon shugaban kasar Zambia

A shekarar 2003 ne aka tuhumi tsohon shugaban Zambia Frederick Chiluba da tsohon shugaban hukumar leken sirin kasar, Xavier Chungu, da wasu manyan jami'an gwamnatinsa da laifin cin hanci da rashawa da ya kai $40m.

Duka mutanen biyu sun musanta wannan zargi suna masu cewa siyasa ce kawai.

Charles Taylor - tsohon shugaban Laberiya

A watan Yunin 2003 wata kotun Liberia ta tuhumi Charles Taylor da aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil adama.

Daga bisani kotun kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ta daure shi bisa laifin tallafawa 'yan twayen da suka karkashe mutane a kasar Saliyo.

Laurent Gbagbo - tsohon shugaban Ivory Coast

An kama tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ranar 11 ga watan Afrilun 2011 sannan aka soma shari'arsa ranar 28 ga watan Janairun 2016 a kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaki da ke Hague.

An tuhumi tsohon shugaban ne da laifin aikata laifukan yaki, zargin da ya musanta, sannan ya ce bita-da-kullin siyasa ce kawai.

Hosni Mubarak - tsohon shugaban Masar

An kama Hosni Mubarak da 'ya'yansa biyu Gamal Mubarak (hagu) da Alaa Mubarak (dama) a shekarar 2011 inda ake zarginsu da almubazzaranci da dukiyar Masar.

Duka mutanen uku sun musanta wadannan zarge-zargen.

Daga bisani wani alkali ya bayar da umarnin sakin tsohon shugaban - matakin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi Allah-wadai da shi.

An hambaras da shi daga kan mulki a shekara ta 2011 bayan wani juyin-juya hali da jama'ar kasar suka yi.

Hissene Habre - tsohon shugaban kasar Chadi

A shekarar 2013 wata kotun da aka kafa a Senegal ta tuhumi tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre bisa aikata laifukan cin zarafin dan adam lokacin mulkin da ya yi tsakanin 1982 da 1990.

Ko da yake ya sha musanta zargin, sannan ya ce kotun ba ta da ikon tuhumarsa.

A karshe kotun ta same da laifi sannan ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.

Mohamed Morsi - tsohon shugaban Masar

An kama Mohammed Mosri bayan da sojoji suka yi masa juyin mulki a daidai lokacin da ya cika shekara guda a kan mulki.

An tuhume shi da laifuka daban daban da suka hada da cin amanar kasa, cin hanci da kuma haka kai da makiyan Masar daga wajen kasar.

Sai dai ya musanta dukkan wadannan zarge-zarge, inda ya ce siyasa ce kawai.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi Allah-wadai da yadda "aka ci zarafinsa" da ma na magoya bayan kungiyarsa ta 'Yan Uwa Musulmi.