Yaki da cin hanci: Buhari bai ce zai taimakawa Ghana ba

Asalin hoton, Bashir Ahmad
Batun cewa Najeriya za ta taimakawa Ghana yakar cin hanci da rashawa a jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce a shafukan sadarwa na Intanet.
A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci bikin cika shekara 61 da samun 'yancin kasar Ghana.
Kuma a wajen bikin, shugaban na Najeriya ya gabatar da jawabi, inda a ciki aka ruwaito ya ce zai taimakawa kasar Ghana yaki da rashawa.
Hakan ya sa wasu 'Yan Najeriya suka shiga shafukan sada zumunta a intanet suna sukar shugaban ta hanyar kalamai da hotunan ban dariya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
"Idan mutum zai baka riga ya dibi ta wuyansa", kamar yadda Sanata Ben Muray-Bruce na jam'iyyar adawa ta PDP daga yankin Niger Delta a kudancin kasar ya wallafa a shafinsa na twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sai dai kuma labarin da aka ruwaito shugaban ya fada ba gaskiya ba ne.
An yi wa jawabin da shugaba Buhari ya gabatar a Ghana fassara ne ta daban a kafofin yada labarai na talabijin da kuma na sadarwa a intanet.
A jawabinsa, Buhari bai ce zai taimakawa Ghana yakar rashawa ba, illa ya ce "Najeriya a shirye take ga duk wani shiri na hadin guiwa domin magance matsalar"
" Zan iya tabbatar wa da mai girma shugaban kasa cewa kana da abokin tafiya kamar yadda na ke sa ido ga duk wani nau'i na hadin kai tsakanin Najeriya da Ghana a kan yaki da rashawa".