'Garuruwan da ake rikici ya kamata Buhari ya je ba manyan birane ba'

Wasu 'yan Najeriya sun ce gara shugaban kasar ya kai ziyara wuraren da ake fama da rikici maimakon ya tsaya a manyan biranen jihohin da zai kai ziyarar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu 'yan Najeriya sun ce gara shugaban kasar ya kai ziyara wuraren da ake fama da rikici maimakon ya tsaya a manyan biranen jihohin da zai kai ziyarar

A Najeriya, a yayin da fadar shugaban kasar ta yanke shawarar shugaba Buhari zai kai ziyara jihohin Taraba da Yobe da Zamfara da Benue da kuma Rivers, jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula, wasu 'yan kasar na cewa duk da sun yi farin cikin jin wannan labari, babu amfanin wannan ziyara matukar shugaban kasar zai tsaya a manyan biranen jihohin.

A wata tattaunawa da daya daga cikin shugabannin kungiyar hadakar kungiyoyin matasa ta arewa CNG, Malam Ashiru Shariff, ya shaida wa BBC cewa, ziyarar ainihin yankunan da matsalar ke faruwa ne dai zai ba wa shugaban hasken gaskiyar abinda ke faruwa.

Malam Ashiru ya ce, yakamata shugaban Najeriyar ya je wuraren da rikice-rikice suka faru domin ganawa da wadanda abin ya shafa ko kuma bangarorin da ke rikici da juna.

Daga ranar Litinin din data gabata ne, shugaban zai fara kai ziyara jihar Taraba, kafin ya zarce zuwa Benue da Yobe da Zamfara da kuma Rivers.

Wasu 'yan kasar ta Najeriya da dama, na ganin cewa shugaban ya yanke shawarar kai wadannan ziyarce-ziyarce ne saboda irin korafi da kuma kiraye-kirayen da aka yi ta masa na nuna masa muhimmanci ziyarar, musamman ma dai bayan da ya halarci daurin auren diyar Gwamnan Kano a ranar Asabar din da ta gabata.

Masu amfani da shafukan sada zumunta a kasar sun soki shugaban na Najeriya da nuna rashin dattako kasancewar bai kai ziyara garin Dapchi ba, inda 'yan bindiga suka shiga makarantar Mata suka sace dalibai 110 a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Haka kuma shugaban ya sha suka saboda rashin kai ziyara a jihohin da suka yi fama da kashe kashen mutane, kamar Benue inda aka kashe mutum sama da 70 a farkon watan Janairu.