Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fara gwajin sabuwar allurar riga kafin zazzabin Typhoid
Ana gwajin wata sabuwar allurar rigakafi kan cutar zazzabin taifod akan yara kanana a wani asibiti da ke kasar Malawi.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta amince da sabuwar allurar rigakafin.
An kuma yi kiyasin cewa cutar taifod ta addabi mutane miliyan 12 zuwa 20 a kasashen duniya musamman a kudancin Asiya da yankin Africa kudu da sahara.