An hallaka 'yan sanda 5 da soja daya a Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, AFP
'Yan sanda biyar da wani soja daya sun rasa rayukansu, a wani samame da suka kai a gabashin birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudun.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito ya ce, 'yan sanda uku sun mutu ne nan take.
Yayin da shi kuma sojan ya rasa ransa ne a lokacin da maharan suke tserewa sun kuma yi garkuwa da jami'an tsaro uku.
Daga bisani aka tsinci gawarsu a bakin hanya, tafiyar kilomita shida tsakanin wurin da ofishin 'yan sandan.
Sanarwar da gwamnati ta fitar ta tabbatar da cewa maharan ne suka harbe jami'an tsaron sun kware a harbi.
Wasu gungun 'yan fashi dauke da makamai da ba a san ko su waye ba, su ne suka bude wuta da sanyin safiyar ranar Laraba a ofishin 'yan sandan.
Kawo yanzu 'yan sandan ba su san dalilin da ya sa barayin suka kawo harin ba. Sai dai rahotanni sun ce barayin sun kai hari wani injin ba da kudi na wani banki wato ATM tare da kwashe kudin ciki.
Da suka kawo hari ofishin 'yan sandan sun yi awon gaba da manyan bindigogi 10 da motar 'yan sanda daya.
Kwamishinan 'yan sandan Afirka ta Kudu Gen Khehla John Sitole, ya sha alwashin zakulo duk inda maharan suka shiga don su fuskanci shari'a, ya kara da cewa: ''ya na matukar bakin ciki kan abin da ya faru, da alhinin mutuwar 'yan sandan da soji guda.''
Tuni 'yan kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu ta shafukan sada zumunta da muhawara.
Wani abokin iyalan daya daga cikin mamatan, ya wallafa shafinsa na facebook cewa: ''Kai hari a ofishin jami'an tsaro barazana ce ga tsaron kasa.''
Ya kara da cewa a halin da ake ciki mutane na zaman dar-dar na rashin sanin halin da za su samu kansu a ciki. Saboda idan har za a kai hari ofishin 'yan sanda a kuma hallaka 'yan sanda, ko wanne dan kasa ka iya samun kansa a irin halin.
Wakilin BBC a kasar Afirka ta Kudu Milton Nkosi, ya ce gabannin kai harin an gudanar da wani bincike da ya gano an samu raguwa matuka ta kisan 'yan sanda da kashi 52 cikin 100 tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994.











