Iceland: Za a hukunta wanda ya yi wa dansa kaciya

Asalin hoton, Getty Images
Wani shugaban addinin musulunci a Iceland, ya yi alawadai da shirin da ake yi a kasar na hana kaciyar maza a matsayin wani yancin da mutane suke da shi na yin addininsu.
Ahmad Saddeeq, wanda limami ne a wata cibiyar raya addini da kuma al'adu a kasar, ya shaidawa BBC cewa, yin kaciya na daga cikin koyin addinin musulunci, dan haka batun hana wa sam bai dace ba.
Wani kudurin doka da ke gaba majalisar dokokin kasar a yanzu, ya tanadi hukuncin daurin shekara shida ga duk iyayen da aka samu da yi wa 'ya'yansu kaciya.
Kasar Iceland, ta zamo kasa ta farko a tarayyar turai da za ta fara bullo da doka a kan daina kaciyar maza.
A cikin kudurin dokar, an bayyana cewa yawanci ana yi wa yaran kaciya ne a gida kuma ba mamaki ana amfani da kayan aikin da ba a tsaftace su ba.
Musulman da suke kasar dai tsiraru ne.











