EFCC ta kama Babachir Lawal

Kamen nasa na zuwa ne bayan kwana daya da tsohon shugaban kasa, Olusegun ya soki gwamnatin kasar kan yaki da cin hanci da rashawa

Asalin hoton, The Guardian

Bayanan hoto, Kamen nasa na zuwa ne bayan kwana daya da tsohon shugaban kasa, Olusegun ya soki gwamnatin kasar kan yaki da cin hanci da rashawa

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nigeria watau EFCC ta ce ta kama tsohon sakataren gwamnatin kasar , Babachir Lawal.

Rahotanni sun ce a jiya Laraba ne jamian EFCC suka capke Mr Lawal.

A kwanakin baya da suka gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya kori Mr Lawal din.

Ya kuma dauki wannan matakin ne bayan kwamitin da ya kafa domin gudunar da bincike kan zargin karkatar da kudaden da aka ware ma 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita, ya same Babachir Lawal da laifi.

A baya ma ,Majalisar datawan kasar ta sameshi da laifi dangane da wannan batu.

Kamen nasa dai na zuwa ne bayan da tsohon shugaban kasar Nigeria, cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da rashin daukar mataki akan mutane da ke da kusanci da shi, wadanda ake zarginsu da almundahana.