Ko fim zai taimaka a daina kyamar mata masu jinin al’ada?

Fim din Pad Man labari ne na gaskiya da wani mutum ya yi gwagwarmaya wajen samar da audugar mata mai saukin kudi a kasar India

Asalin hoton, Mr Murunganantham

Bayanan hoto, An shirya fim din Pad Man domin isar da sako a kan muhimmancin samar da audugar mata ga mata masu jinin al'ada a kasashen duniya

Pad Man, Labari ne na wani mutum da ya shafe shekara 20 yana gwagwarmaya domin ya saya wa matarsa audugar al'ada, amma daga karshe ya kare da taimakawa rayuwar miliyoyin mata a fadin duniya.

Arunachalam Muruganantham, shi ne ainihin sunan mutumin da ya yi wannan gwagwarmayar kuma ya fito ne daga kudancin kasar India.

Jarumin fina-finan Bollywood na India Akshay Kumar, ya fito a matsayin Muruganantham a cikin fim din da aka yi wa lakabi da Pad Man.

Fim din Pad man, fim ne na barkwanci kuma an yi sa ne da nufin wayar da kan mutane a kan su dai na kyamatar mata idan suna jinin al'ada.

Fim din za a yi shi ne a kan muhimmancin audugar mata

Asalin hoton, SONY PICTURE

Bayanan hoto, Akshay Kumar shi ne zai fito a cikin fim din Pad Man

Labarin fim din ya samo asali ne tun a shekarar 1998, lokacin da wani sabon ango wato Muruganantham ya fuskanci amaryarsa Shanti na boye masa wani abu.

Mista Muruganantham, ya ce ba wani abu ba ne illa wani tsumma mai dauda wanda za ta yi amfani da shi a lokacin da take al'ada.

Mista Muruganantham, ya ce ko da goge babur dinsa ba zai iya yi da tsumman da take amfani da shi ba.

Wannan dalili ya sa Mista Muruganantham ya shiga gwagwarmayar samar da wata na'ura mai saukin kudi da za ta iya yin audugar mata da ke kira pad a turance.

Ba tare da sanin makwabtansa ba ya rinka gwajin sabuwar na'urar da ya kirkira ta hanyar saka wani kamfai a jikinsa tare da sanya audugar da ake yi a gida inda a hankali jinin akuya da aka saka a cikin wata roba da ya daura a jikinsa ke diga a hankali a kai.

Mr Muruganantham, ya ce" Na yi wannan gwaji ne bayan da na ga wannan tsumman mai tsananin datti da matata ke amfani da shi a matsayin kunzugu idan tana al'ada, daga nan ne na yanke shawara zan saya mata audugar zamani na ba ta a matsayin kyauta ta musamman.

"Na shiga wani shago sai mai shagon ya ba ni audugar a matsayin kayan da aka yi fasa kaurinsu. Saboda ina son na san kwakwaf sai na bude ledar audugar na ga yadda ta ke, abin takaicin shi ne yadda ake sayar da ita da tsada".

Tun daga wannan lokaci ne Mista Muruganantham, ya shiga binciken yadda zai samar da auduga mafi sauki ga mata, hakan ya sa ya fara wannan gwaji a gida.

Yin jinin al'ada a cikin talauci na sanya mata miliyan 300 a India cikin halin kaka-ni-kayi wajen samun audugar da za su yi amfani da ita, wanda hakan ke sa da yawa daga cikinsu kamuwa da cutuka ko rashin haihuwa kai wani lokaci ma har da rasa rai.

Mista Muruganantham, ya yi amfani da wannan matsala da matan kasarsa ke fama da ita, ya fara nazari a kan audugar matan da ake sarrafawa a kamfanonin kasashen waje da sauraron ra'ayin jama'a da kuma amfani da nafkin, daga karshe har ya samar da ta sa audugar mai saukin farashi.

Mista Muruganantham ya ce " Ina son wadanda za su gwada audugar da na yi su ba ni sakamako, to amma ko matata ta ki ta gwada".

Mr Murunganantham shi ne ya samar da audugar mata mai rahusa

Asalin hoton, Mr Murunganantham

Bayanan hoto, Mista Murunganantham shi ne ya samar da audugar mata mai rahusa

Mista Muruganantham, ya ce "a lokacin da na yi gwajin da kai na na sanya wannan kyallen a jikina na sa jinin akuya a cikin roba yana disa kadan-kadan, matata ta guje ni, haka mahaifiyata ma ta gudu, yayin da sauran al'ummar kauyenmu kuma suka zaci ko na samu cutar da ake dauka daga jima'i ne.

Duk da wannan kalubale Mista Muruganantham, ya ci gaba da jajircewa wajen samar da audugar.

A shekarar 2006, ya kaddamar wa da wani kamfani wanda ke aikinsa ba don riba ba wato Jayaashree Industries audugarsa.

Daga nan wannan kamfani ya ba shi na'urorin da zai rinka samar da audugar a kan farashi mai sauki ga kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyin mata a sassan kasar ta India.

A yanzu matan India miliyan 40 na amfani audugar Mista Muruganantham, kuma akwai shirin cewa za a kai irin wadannan na'urorin sarrafa audugar zuwa kasashen Kenya da Najeriya da Sri Lanka da kuma Bangladesh.

Twinkle Khanna ita ce mataimakiyar mai shirya fim din Pad Man

Asalin hoton, Akshay Kumar

Bayanan hoto, Twinkle Khanna ita ce mataimakiyar mai shirya fim din Pad Man

Twinkle Khanna, wadda ita ce mataimakiyar mai shirya fim din Pad Man, ta karanta labarin Mista Muruganantham a shafin sada zumunta ne anan ne labarin ya ja hankalinta saboda ganin irin nasarar da ya samu.

Twinkle Khanna, ta ce " Ina ganin wannan labari ne mai ma'ana da ya kamata ya isa ga gidajen mutanen India da ma sauran kasashen duniya, saboda ina ganin matsalar kyamatar mata masu jinin al'ada ba kasar India ce kadai ke fuskanta ba, har da sauran kasashen duniya."

Wannan dalili ya sa Mrs Khanna, ganin ya kamata a yi fim a kan labarin Mr Muruganantham.

Ba tare da ba ta lokaci ba, mai gidanta Akshay Kumar, ya sanya hannu a kan cewa shi zai fito a cikin fim din a matsayin Mista Muruganantham.

Akshay Kumar ya shahara a fina-finan Bollywood

Asalin hoton, Akshay Kumar

Bayanan hoto, Akshay Kumar ya shahara a fina-finan Bollywood

Akshay Kumar, wanda ya saba fitowa a cikin fina-finan Bollywood ya ce zai yi wannan fim din domin kira ga mahukunta a kan muhimmancin samar da audugar mata ga mata masu jinin al'ada a India da ma duniya baki daya.

Akshay Kumar, ya ce " Shawo kan matsalar kyamatar mata na da matukar muhimmancin gaske, don haka fim din Pad Man da zan yi zai isar da sakwanni masu matukar muhimmancin gaske."

Yanzu dai Mista Muruganantham, wanda ya yi suna a kasashe kamar Amurka da Jamus saboda yana kai audugar sa can, ya ce ya yi wannan kokari ne na samar da auduga mai saukin farashi domin sanya kasarsa ta India ta zamo kasar da ake amfani da audugar mata 100 bisa 100 a duniya.

Kuma ya ce yana fatan wannan yunkuri na sa zai sa sauran kasashen duniya amfani da audugar saboda babu tsada, wanda hakan kuma zai sa a daina kyamatar mata idan suna jinin al'ada.