Sheikh Dahiru Bauchi ya soki gwamnati kan rikicin Benue

Sheikh Dahiru Bauchi

Asalin hoton, Sheikh Dahiru Bauchi

Bayanan hoto, Rashin filayen kiwo ne ya haifar da rikicin makiyaya da manoma, in ji Sheikh Dahiru Bauchi

Shahararren malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya soki gwamnonin kasar da suka yi ikirarin haramta kiwo a jihohinsu.

Shaihin Malamin ya shaidawa BBC cewa dole ne dabbobi su ci abinci kuma ba yadda za a raba Dan Adam da dabba.

"Duk gwamnan da ya ce zai hana kiwo, to sai ya tafi sahara a can ya yi gwamna inda ba mutane ba dabbobi", a cewar Sheikh Dahiru Bauchi.

Ya kuma kara da cewa duk wanda ya ce zai hana kiwo, to zai hana zaman lafiya. A cewarsa "Idan kana da dabbobi dole ne ka ciyar da su kamar yadda kake ciyar da iyalanka".

Babban Malamin dai na wannan bayanin ne a daidai lokacin da ake zargin Fulani makiyaya da kisan mutane da dama a jihar Benue, zargin da suka sha musantawa.

Tuni dai gwamnatin Jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ta haramta kiwon sake a fadin jihar, saboda rikicin na makiyaya da Manoma.

Amma Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ba zai yiyu ba ace mutum ya zauna da dabbobi kuma a hana shi abincin da za su ci da sha ba.

A cewar Malamin, da ace makiyaya suna da burtalin shiga da fita, yana da tabbacin cewa makiyayan ba za su su shiga gonakin mutane ba haka kawai.

Masu cewa ba za su yadda su bayar da filayen da suka gada daga iyaye da kakanni ba don a yi wurin kiyo da burtali, a cewar Malamin "wannan maganar banza ne".

"Keta dokokin Najeriya ne kuma take hakkin Dan Adam na Najeriya ne".

Ya kara da cewa dokar kasa ta bayar da dama ga dan Najeriya ya zauna duk inda ya ga dama, ba wanda ya isa ya hana shi, Kuma ya mallaki kowace irin dukiya yake so babu mai hana shi.

A cikin makon nan ne dai fadar shugaban kasa ta gana da gwamnan Benue da sauran masu ruwa da tsaki a jihar domin lalubo hanyoyin magance rikicin makiyaya da manoma.

Wasu dai na ganin kin bin doka da kuma barin abubuwa su lalace ba tare da daukar matakin da ya da ce a kai ba ne suke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Amma Gwamnatin Najeriya ta sha musanta cewa sakacinta ne yake haifar da wannan rikici.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce hana wa makiyaya rayuwarsu ta kiwon dabbobi ne ya tursasa masu daukar makami.

Sannan a cewarsa, duk rashin filayen kiwo ne ya haifar da rikicin makiyaya da manoma, saboda Manoma suna nome fulayen kiwo da burtali suna hanawa makiyaya samun wurin kiwo.

Shaihin Malamin ya yi kira ga gwamnati ta samar wa makiyaya da burtali na shiga da fita domin dabbobinsu da kuma filayen kiwo da Dam Dam tare kuma da yin kira ga makiyaya su kaucewa daukar doka a hannunsu, domin samun zaman lafiya a kasa.

Rikicn Makiyaya da Manoma a Najeriya
Bayanan hoto, Gwamnatin Benue ta haramta kiwon sake a fadin Jihar

Rikicin makiyaya da manoma musamman a jihohin tsakiyar Nageriya na daga cikin manyan kalubalen tsaro da kasar yanzu ke fuskanta, baya ga rikicin Boko Haram, da matsalar sacewa da garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi kasar.

Rikicin na makiyaya da manoma ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a jihohin arewacin Najeriya.