Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya ta cafke masu halartar auren 'yan luwadi
'Yan sanda a Saudiyya sun ce sun cafke wasu matasa da dama wadanda suka fito a wani faifen bidiyo daya nuna kamar sun halarci aure ne na 'yan luwadi.
Faifen bidiyon ya nuna mazaje na tafiya kafada da kafada da juna akan darduma ana watsa musu furanni a wani budadden wuri.
Bidiyon ya nuna kamar daya daga cikin su na sanye da doguwar riga kamar irin wanda Ango da Amarya ke sanyawa a lokutan bukin aure.
Sai dai a ranar Litini 'yan sanda a birnin Makkah sun ce sun gano wadanda ke sanye da suturar Ango da Amaryar da kuma sauran mutanen da ke faifen bidiyon.
An kuma tsare su inda aka gabatarwa masu shigar da kara na gwamnati batun.
Kawo yanzu dai jami'an 'yan sanda ba su fitar da sunayen mutanen ba da kuma tuhumar da za su iya fuskanta.
Saudiyya dai na bin tafarkin shari'ar musulunci ne kuma alkalai na amfani da tanade tanaden shari'ar wajen zartar da hukunci kan laifuffuka kamar lalata da luwadi da sauran su.
'Yan sandan sun ce suna kyautata zato cewa an yi "auren 'yan luwadin" ne ranar Juma'a a wani wurin shakatawa a kasa mai tsarki, al'amarin da ya yi matukar ba jama'a mamaki.
Ko a watan Fabrairun 2017 Saudiyya ta kame wasu 'yan kasar Pakistani 35 cikin su har da wasu mata-maza.
Daya daga cikin su mai suna Meeno Baji, ta mutu a lokacin da ake tsare da su kuma 'yan uwanta sun ce an ga alamun azabtarwa a gawarta, sai dai jami'ai sun ce ta mutu ne sakamakon bugun zuciya.