Sufeton 'yan sandan Nigeria ya koma Benue

Benue

Asalin hoton, FACEBOOK NPF

Bayanan hoto, Sufeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya tare a Benue

Sufeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya koma da zama a jihar Benue da ke tsakiyar kasar domin magance rikicin manoma da makiyaya.

A wata sanarwa, kakakin rundunar 'yan sandan Jimoh Moshood ya ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bukaci sufeton na 'yan sandan ya gaggauta komawa Benue domin hana bazuwar rikicin.

Shugaban 'yan sandan ya koma Benue ne tare da wasu rundunonin 'yan sanda na musamman guda biyar domin tabbatar da tsaro da bin doka da oda.

Kimanin mutane 20 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu dubu arba'in suka bar muhallansu a rikicin baya-bayan nan da ya auku a kananan hukumomin Guma da Loko a jihar ta Benue.

Yanzu jimillar rundunonin 'yan sanda 10 ne aka tura kan rikicin na manoma da makiyaya a Benue.

Cikin matakan da rundunar 'yan sandan ta ce zata ci gaba dauka sun hada da sintiri da jirage masu saukar ungulu da kuma a motoci.

SP Almustapha Sani jami'i a ofishin hulda da jama'a na hedikwatar rundunar 'yan sanda da ke Abuja, ya shaidawa BBC cewa tuni sufeton na 'yan sandan ya koma Benue da zama domin bin umurnin shugaban kasar.

Sannan ya ce komawar shugaban 'yan sandan a Benue, wani karin kaimi ne ga jami'ansa.

Benue

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihohin arewa da dama na fama da matsalar rikicin makiyaya da Manoma a Najeriya.

Baya ga matsalar Boko Haram da ake ci gaba da fuskanta a arewa maso gabashi, jihohi da dama ne na arewa ke fuskantar matsalar rikicin makiyaya da manoma da sace sacen jama'a.

Sama da shekara 10 ke nan a Najeriya, ake fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma kan batun filayen kiwo.