Yadda bahayar fasinjoji ta sa jirgin sama saukar gaggawa

Jami'ai sun ce wani jirgi da ya dauko fasinjoji sama da 200 daga Chicago zuwa Hong Kong ya karkata akalarsa inda ya ya da zango a Alaska bayan da biyu daga cikin bandakunansa suka gurbace da bahaya.

An tilasta wa jirgin na United Airlines ya da zango a inda bai shirya ba a Anchorage a yammacin Alhamis sakamakon yadda wani fasinja ya yi bahaya a ko ina.

'Yan sanda sun ce mutumin mazaunin Amurka ne dan asalin Vietnam.

Ba a gano musabbabin faruwar hakan ba.

"Mun samu rahoton fasinjan da ya bata bandakunan da bahayan da ya yi," in ji mai magana da yawun 'yan sandan filin jirgin Anchorage Lt Joe Gamache.

Lt Gamache ya kara da cewa, "fasinjan mai shekara 22 wanda ba a a bayyana sunasa ba, ba a tuhumshi da karya wata doka ba."

'Yan sanda sun saka wa mutumin ankwa a filin jirgin Anchorage kuma suka fitar da shi daga cikin jirgin.

Sun shaida wa gidan talabijin na Anchorage cewa sun kai shi asibiti don duba lafiyar kwakwalwarsa, bayan da aka yi masa tambayoyi ta hanyar tafinta.

A wata sanarwa da kamfanin jirgin ya bayar, jirgin mai kirar UA895 na dauke da fasinja 245 a lokacin da ya karkata akalarsa sakamakon abin da fasinjan ya yi.

Sanarwar ta kara da cewa an tanadar wa da fasinjojin dakuna a otel.