Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Lawal Kaita ya rasu

Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun ce fitaccen dan siyasar a Najeriya, ya rasu ne a yau Talata a wata asibiti a birnin Tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru tamanin da biyar a duniya.

Kaita ya yi gwamna ne a inuwar jam'iyar NPN a tsohuwar jihar Kaduna a 1983 kafin sojoji su yi wa Shagari juyin mulki.