Yadda wata 'yar Indiya ke amfani da tsiraici don nema wa mata 'yanci

Asalin hoton, Claudia Pajewski
Ya ya za ka dauki wata mace mai kananan shekaru da ta fara wasa na kwaikwayo tsirara.
A kasar kamar Indiya mai halin 'yan mazan jiya, da wuya ka sami irin haka. Amma ga marubuciyar wasannin kwaikwayo kuma 'yar wasan na kwaikwayo, jikinta shi ne makami babba da take amfani da shi wajen samar wa mata 'yanci.
Ta fada wa Ayeshea Perera ta BBC abin da ke bata karfin gwuiwa.
"A lokacin da na fara yin wasa tsirara a bainar jama'a ...na ji dadina.
"Akwai wani mai daukar hoto a wurin, kuma idan ki ka kalli bidiyonsa za ki ga wani wuri a ciki inda hoton ya yi tsalle bayan da aka kunna hasken lantarki saboda faduwa da baya da ya yi a sanadiyyar gani na tsirara.
"Kuma can sai wani dan kallo ya ce 'Ai yo!'," in ji Malika Taneja, tana dariya.
Duk da yake wannan ne abin da mutane suka fi yin magana akai, amma 'yar shekara 33 da haihuwar ta ce ba shi ne dalilin yin wasan da take yi ba.
Wasan me suna Thoda Dhyan Se (wato A dan yi a hankali) wasa ne da take so ya sosa zukatan mutane game da ko irin kayan da mata ke saka wa na da nasaba da harin da ake kai musu.

Asalin hoton, Claudia Pajewski
"Yaya ake watsa taron mutane? Bijirewar mutum guda kawai ake bukata".
Ta ce, "Mutum guda na iya shiga tsakiyar jama'a ya kuma dakatar da ita."
A wani wasa da ta shirya - inda ta fito tsirara tana kallon 'yan kallonta na tsawon minti takwas - misali ne na yiwuwar hakan.
A kowane wasa da ta shirya a shekaru hudu da suka gabata, ta ce masu kallo kan yi tsit a mintunan farko, shirun da "kan cika dakin."
A wannan lokacin da Ms Taneja ke kallon da masu kallonta, ta kan lura duk da cewa an fi ta yawa, amma ta fi su karfi a lokacin.
Amma yin wasa tsirara na damunta sosai.
Ba ta barin a shiga da wayoyin hannu ko wani abin daukar hoto cikin wurin da take wasa.
Kuma a shekaru hudun da ta dauka tana wasa, ba a taba samun hoto ko bidiyo daya da ya nuna tsiraicinta ba.
Bayan da wasan ya cigaba, Ms Taneja kan saka wasu kaya a jikinta, har ma ta kan saka hular kwano, inda ta ke sanar da masu kallonta cewa a matsayinta na mace, dole ta "yi taka tsantsan".

Asalin hoton, Claudia Pajewski
Ta kara da cewa: "Mata sun fahimci dalilin wannan wasan nawa, amma yana da muhimmanci da maza suka ce ya bude musu ido."
Dalilanta na yin wannan wasa ita kadai sun hada da irin rayuwar da ta ke yi ne. Ms Taneja ba ta da miji, ita kadai take zaune a gidanta, kuma bata aiki irin na yau da kullum - wato irin wanda ake farawa daga karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma.
Ta yarda cewa nasarar da ta samu, da kuma kudaden da take da su sun taimaka wajen bata karfin zuciyar ci gaba da yin wasannin.
"Babu wanda ya taba sukar yadda nake tafiyar da rayuwata - ko babana, ko 'yan uwana," in ji ta.

Asalin hoton, Claudia Pajewski
Idan mace ta ce a'a ko sau daya ne, to lallai ta ba da gudummuwarta wajen samun daidaito tsakanin jinsuna.
A 2012 kasar Indiya ta shaida haka. Wani lamari na fyade da aka yi wa wata mata ya zaburad da dubban mata, inda suka fito suna cewa sun gaji da wannan halayya.
Bayan wannan fitowar ce aka sami sauyi wajen sabbin dokoki da kasar ta kaddamar domin maganin lamarin.

Asalin hoton, Claudia Pajewski
Amma wasu mata na ganin ba zata iya wadannan wasannin ba ma sam-sam da tana da kiba.
Sai ta ce "Ban san amsar wannan maganar ba. Wannan jikin shi ne nawa. Amma zan gaya musu cewa 'Ina fata'.
Wannan labarin na daga cikin jerin labarai game da matan Indiya masu yakin kawo daidaito tsakanin jinsuna.











