Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Goodluck Jonathan ya yaba wa Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar cika shekara 75 a duniya, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.
A ranar Lahadi ne shugaban zai cika shekara 75 da haihuwa.
Mista Jonathan ya yaba wa shugaban inda yake cewa: "tarihi ba zai taba mantawa da jajircewarsa da kuma kokarin da yake wajen samar wa kasar nan kyakkyawar makoma ba."
Daga nan sai ya ce yana taya 'yan uwa da abokan arzikin shugaban murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A watan Maris din shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben kasar, bayan samun nasara a kan babban abokin hamayyasa Mista Goodluck Jonathan wanda ke kan karagar mulki a lokacin.
Karanta wadansu karin labarai