Nigeria: Gobara ta cinye shaguna a kasuwar Panteka

Wata mummunar gobara ta cinye shaguna da dama a kasuwar Panteka da ke Tudun Wada a jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Wakilin BBC wanda ya ziyarci kasuwar ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Juma'a inda ta haddasa asarar kayayyaki da dukiyoyi kafin a shawo kanta.

Tsohuwar kasuwar Panteka dai kasuwa ce da ake sayar da Katako, karafuna da sauran kayan gine gine.
Wani jami'ai a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna SEMA ya ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike don gano masabbabin tashin gobarar.

Asalin hoton, KADUNA GOVERNOR
Tuni gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ziyarci kasuwar don jajantawa wadanda suka yi asara.
Matsalar barkewar gobara dai na neman zama tamkar ruwan dare a kasuwannin Nigeria inda a kowace shekara take haddasa barna mai dimbin yawa.







