An kashe 'yan sanda a Adamawa

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce wasu 'yan bindiga sun kashe jami'anta a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Othman Abubakar, ya shaida wa BBC cewa takwarorin nasa sun gamu da ajalinsu ne a garin Dowaya na yankin karamar hukumar Numan lokacin da suka je aiki.
A cewarsa, 'yan sandan sun tafi yankin ne domin gudanar da bincike game da zargin mallakar miyagun makamai ba bisa ka'ida ba da ake yi wa wasu Fulani makiyaya amma sai ake zargin makiyayan sun far ma jami'an na tsaro.
Wani limamin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa tuni mazauna kauyen da ma kauyukan da ke kewaye da shi suka soma tururuwar fice wa daga cikinsa da ma saboda tsoron abin da ka je ya komo.
Sai dai rundunar sandan jihar ta bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu.
Garin na Numan dai ya yi fama da rikici a watan jiya, inda arangama tsakanin kabilun Bacama da Fulani ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 20.







