'Za mu iya harba sabon makami mai linzami kan Amurka gaba daya'

Asalin hoton, Reuters
Koriya Ta Arewa ta ce ta samu nasarar yin gwajin wani sabon makami mai linzami (ICBM) wanda zai iya kaiwa ga baki dayan kasar Amurka idan aka harba shi.
Gidan talbijin na kasar ya ce a yanzu Koriya Ta Arewa ta cimma burinta na zama mamallakiyar makami mai linzami.
An kaddamar da makami mai linzamin ne samfurin Hwasong-15, wanda aka bayyana shi da mafi karfi a ranar Laraba da sassafe.
Ya sauka a tekun Japan amma ya yi tafiya mafi tsawo da duk wani makami mai linzami da Koriya Ta Arewa ta taba gwajin harba shi a baya.
Gwajin, wanda ya bijirewa takunkumin kasa da kasa da aka kakabawa shirin makaman Koriya Ta Arewan, ya sha suka daga kasashen duniya, inda har Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa.
Koriya Ta Kudu ta mayar da martani ta hanyar yin atisayen harbe-harbe, inda ta kaddamar da daya daga cikin makamai masu linzaminta ita ma.

Asalin hoton, EPA
Mene ne ainihin abin da Koriya Ta Arewa ke cewa?
An sanar da labarin kaddamar da harin ne a gidan talbijin na kasar da tsakar rana, da kuma a wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na kasar KCNA ya fitar.
Koriya Ta Arewa ta ce makami mai linzamin ya kai nisan kilomita 4,475 a sararin samaniya, ya kuma yi tafiyar kilomita 950 cikin minti 53, kamar dai yadda rundunar sojin Korita Ta Kudu ta kiyasta.
Sai dai a wannan karon makamin da aka harbadin bai bi ta sararin samaniyar Japan ba kamar yadda aka sha yi a baya, ya kuma sauka ne a nisan kilomita 250 daga gabar tekun kasar, a cewar jami'an kasar Japan.
Koriya Ta Arewa dai ta sha cewa makaminta zai iya kai wa Amurka, amma wannan ne karo na farko da ta ce za ta iya yin hakan da wani sabon samfurin makami mai linzami da ta kaddamar.
Kamfanin dillancin labaran kasar KCNA, ya kara da cewa shugaban kasar Kim Jong-un wanda shi ne ya sanya hannu don kaddamar da makamin, ya ayyana cike da alfahari cewa: 'a yanzu mun kai ga cimma gagarumar nasara wajen kafa tarihi na zama kasar da ta mallaki makami mai linzami."
Rahoton ya ce: 'a matsayinta na mamallakiyar makami mai linzami kuma kasa mai son zaman lafiya, Koriya Ta Arewa za ta yi duk wani kokari don kare da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya."
Rahoton KCNA din ya kara da cewa, kasar na kera makamai masu linzami ne saboda kare kanta daga 'mulkin danniyar Amurka' da kuma bata mata suna da shirinta na makami mai linzami.
Shin makamin na iya kai wa Amurka da gaske?
Wani bincike da wata kungiyar masana kimiyya ta Amurka ta yi ya nuna cewa makami mai linzamin na iya tafiyar fiye da kilomita 13,000, ta yadda hakan zai sa ya iya kai wa ga illahirin kasar Amurka.
Sai dai duk da haka binciken ya kara da cewa, makami mai linzamin ba zai iya daukar makamai da yawa a kansa har ya yi tafiya mai nisan zango irin haka ba.
Amma Koriya Ta Arewa ta ce sabon makamin samfurin Hwasong-15 zai iya kai wa ko ina a Amurka dauke da wasu tarin makaman a kansa.

Yaya duniya ta ji da wannan gwaji?
Kafin Koriya Ta Arewa ta fitar da sanarwa, sakataren tsaro na Amurka James Mattis ya ce gwajin makamin ya fi duk wanda aka taba yi a baya muni, ya kuma ce wannan barazana ce ga duniya baki daya.
Wannan gwaji dai shi ne na baya-bayan nan a gwaje-gwajen makamai da Koriya ke yi wanda ya jawo fargaba sosai, ganin yadda Koriyar take biris da sukar da take sha, take kuma ci gaba da shirinta na makami mai linzami.
A watan Satumba ne Koriya Ta Arewa ta kaddamar da wani gwajin makami mai linzami, kuma a cikin watan ne ta kaddamar da irin wannan gwaji har sau shida.











