Me ya sa Nigeria ke son cire shingayen 'yan sanda a tituna?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Amina Yuguda
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wadda ta lashe gasar Komla Dumor ta BBC
Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba da umarnin cire dukkan shingayen binciken 'yan sanda a fadin kasar da gaggawa.
'Yan Najeriya da yawa za su yi maraba da wannan labarin domin galibi shingayen tamkar hanyar damar karbar na goro ne daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki.
Amman sanarwar 'yan sandan ta ce an dauki matakin ne domin a rage lokacin da ake batawa a shigayen binciken da kuma saukaka yadda ake gudanar da kasuwanci.
Me nene ke faruwa a shingayen bincike?
Haduwa da dan sanda a hanya ka iya gajiyar da mutum.
Bindigar Ak47 da suke sabewa a kafada ba ta iya kwantar wa mutum hankali cewa yana cikin tsaro yadda yadda ya kamata.
Yawanci 'yan sanda maza ne, kuma za su bukaci mutum ya bayyana kansa ya kuma fitar da lasisin tukinsa.
Sannan za su nemi su dubi wajen duba kayan mutum.
Daga nan za su tabbatar da cewar kana da dukkan abin da doka ta tanada - na'u'rar kashe wuta a ko wacce mota, da wata alamar da ake sakawa a hanya idan mota ta baci, da inshora, da takardar cancantar mota a kan hanya da kuma sauran takardu.
Duk abin da aka rasa ka iya sa a bai wa mutum zabi tsakanin bin dan sandan zuwa caji ofis ko kuma ba da na goro domin ya taimaka a kashe wutar matsalar nan take.
Ko kana da cikakkun abubuwan da ake bukata, wannan ba ya nufin za ka iya ci gaba da tafiyarka.
Jami'in 'yan sandan zai tambaya in kana da 'abin da za ka bai wa yaran', ko kuma ya nuna maka irin zafin da ake yi (saboda haka yana bukatar kudin shan ruwa).
Wannan ba wani abun da ke faruwa jifa-jifa ba ne, ya zama ruwan dare ta yadda har 'yan barkwancin Najeriya sun sha yin shaguben yadda 'yan sanda ke neman na goro.
Me ya kamata a gujewa a shingen bincike?
Amsa waya a wurin shingen bincike ka iya janyo karin bata lokaci.
Jami'an tsaro ba sa jin dadi su ga mutane suna waya a gabansu.
Lamarin ka iya kamari idan ka nemi ka dauki bidiyon abin da ke faruwa a wurin.
Ba sa lamuntar a dauke su a bidiyo.
A shekarar 2013 an kori Sajen Chris Omeleze bayan wani mutum ya dauki hoton bidiyonsa yana kokarin karbar na goro a filin saukar jirgi na Legas.
Mutumin ya wallafa bidiyon a Intanet.
Ta yaya za ki gane shingen da aka kafa bisa doka?
Babu wata takamammiyar hanya ta bambanta tsakanin shingen gaske da kuma hanyar kwace wa mutane kudi.
Za ki iya ganin durom da launin 'yan sandan Najeriya - shudi da dorawa da kuma kore- a tsakiyar hanya.
Da daddare hasken tocila ne kawai zai nuna maka cewar akwai shingen bincike a wurin.
Idan ka yi rashin sa'a kuma, zai iya kasancewa 'yan fashi ne.
Yayin da aka gindaya wasu shingayen domin kama masu laifi, sauran shingayen hanyoyi ne na samun kudi daga 'yan sanda masu karbar na goro.
Yawanci wadannan na tasowa ne da dare da karshen mako.
Shugaban 'yan sandan ya ba da umarnin cewar 'yan sanda su saka kayan aikin da ke dauke da sunayensu da lambobin aikinsu.
Saboda haka bincike a shafin 'yan sandan zai iya taiamaka wa wajen gano 'yan sandan domin a kai kararsu.
Adadin cin hanci?
Alkalluman hukumar kididdiga ta Najeriya kan cin hnaci da rashawa na shekarar 2017, sun ce kashi 32 cikin 100 na 'yan Najeriya da suka mallaki hankalinsu wadanda suka yi mu'amala da ma'aikatan gwamnati sun ce an tamabaye su na goro.
Hukumar kididdiga ta kasar NBS, ta ce an biya jumullar naira miliyan 82 naira ga jami'an gwamnatin Najeriya a wata 12 da suka wuce.
Wannan na daidai da cin hanci daya ga mutum daya a ko wacce shekara.

Asalin hoton, AFP
Cin hancin da ake nema daga direbobi ya kan kai naira 20.
Direbobin manyan motoci da tasi su ne aka fi karbar na goto a wajensu.
Ba kasafai irin wadannan mutanen ke kalubalantar hukumomi ba kuma suna ba su da lokaci, saboda haka sun gwammaci su biya cin hanci.
Rahoton kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2013 ya ce kashi 92 cikin 100 suna ganin 'yan sanda sun yi dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa.
Shin hana kafa shingen binciken zai yi nasara?
Wannan ba shi ne yunkurin farko na hana kafa shingen bincike a Najeriya ba.
A shekarar 2012, shugaban 'yan sandan lokacin Mohammed Dahiru Abubakar, ya ba da irin wannan umarnin, kuma an dauke shigayen bincike 3,500.
Duk da haka, shingayen sun koma inda aka cire su.
Wannan sabon umarnin wani yunkuri ne inganta gamsuwar mutane da 'yan sanda.
Sanarwar ta ce an tura wasu tawagogi na musamman domin domin kamawa da bincike da kuma hukunta duk wani dan sanda da ya saba wa wannan umarnin.
Yanzu ya zama dole ga ko wacce rundunar 'yan sanda ta nemi yardar sufeto janar na 'yan sanda kafin ta kafa shingaye.
Wannan daya ne daga cikin matakan da sufeto janar na 'yan sanda ya dauka domin ya inganta mutuncin 'yan sanda.
Amman zai dauki lokaci mai tsawo tare da kwararan dalilai kafin yawancin 'yan Najeriya su yarda da taken da ake rubutawa a ofisoshin 'yan sanda: "Dan sanda abokinka ne."













