Bikin kafa Saudiyya ya kawo gwamutsa mata da maza

Saudi women in stadium for first time

Asalin hoton, Reuters

A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasanni don bikin zagayowar ranar 'yancin kan Masarautar Saudiyya.

Filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh babban birnin ƙasar, ya maƙare da ɗaruruwan matan da suka yi ɗango don cin wannan gajiya.

An ga mata a wasu lokuta ma cakuɗe da maza a kan kujeru suna karkaɗa tutocin Saudiyya albarkacin murnar ranar kafa Saudiyya.

Rahotanni sun ce bukukuwan wani yunkuri ne na gwamnatin Sarki Salman don yauƙaƙa alfahari da ƙasa da kuma inganta matsayin rayuwar Sa'udi.

A wannan mako ne, Saudiyya ke shagulgulan cika shekara 87 da kafuwarta a matsayin ƙasa.

Akasari dai filin wasan Sarki Fahad wanda ya saba karbar bakuncin manyan karawar wasannin kwallon kafa, maza ne zalla ke halartarsa bisa tsarin hana gwamutsuwa tsakanin jinsuna a Saudiyya.

Saudi women in stadium for first time

Asalin hoton, Al Arabiya

Jaridar Arab News ta ce tarukan na cikin shagulgula na baya-bayan nan da gwamnati ke daukar nauyi a wani bangare na Burin garambawul nan da shekara ta 2030 wanda kasar ta kaddamar shekara biyu da ta gabata.

Ta ce manufar hakan ita ce baza komar tattalin arzikin Saudiyya ta yadda kasar za ta rage dogaro a kan man fetur.

Sarakunan Saudiyya sun fara garambawul a bangarorin da a baya fage ne kawai na malamai ciki har da ilmi da dokoki.

An kara bukukuwan murnar tunawa da ranar kafa Saudiyya, wanda a baya malaman addinin musulunci ke sukar lamiri da cewa yana zagon kasa ga shaukin addini.