Yaron mota ya yanka dalibin da ya so yi wa fyade a India

An kama manyan jami'ai biyu a wata makaranta da ke lardin arewacin Indiya, wadanda ake zargin suna da hannu a kisan da aka yi wa wani dalibi mai shekara takwas.

Wani dan sanda a Gurgaon da ke kusa da Delhi ya ce, makarantar ta gaza kare dalibin daga wani karen-motar makarantar, wanda ake zarginsa da yi wa yaron yankan rago a ranar Juma'a, bayan da ya yi yunkurin yin lalata da shi da karfi.

Jami'ai sun ce, a ranar Juma'a ne aka kama shi bayan da ya amsa laifin.

Sai dai makarantar ta musanta rashin tsaron da aka ce tana fama da shi inda aka kashe yaron.

A halin da ake ciki yanzu, kotun kolin kasar ta amince ta saurari karar ta bakin mahaifin yaron, tare da neman gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin jihar Haryana, inda Gurgaon yake da zama ta ce, ba sa kalubalantar bukatar iyayen yaron, amma suna bukatar bai wa hukumomin kasar lokaci don su gudanar da bincike.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Gurgaon Ravinder Kumar ya shaida wa BBC cewa, an kama wani babban jami'i da kuma shugaban makarantun Ryan na arewacin Indiya a kan gaza samar wa da daliban tsaro.

Ya kara da cewa, binciken farkon da suka fara yi ya nuna cewa makarantar ta gaza bin tsarin shawarwarin da gwamnatin ta bayar.

Sai dai hukumar makarantar ta musanta zargin.

Ryan Pinto shi ne shugaban kungiyar makarantun ya ce, ba za a kama makarantarsa da kuma ma'aikatanta ba.