Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
India: Kotu ta haramta saki uku a jere
Kotun kolin India ta dakatar da al'adar sakin mace take-yanke mai cike da takaddama tsawon wata shida, inda ta nemi gwamnati ta yi doka a kan batun.
An sa ran cewa kotun za ta yanke hukunci k'ad'aan kan wannan al'ada, da ta ba wa miji damar rabuwa da mace da zarar ya furta saki sau uku.
Kotun kolin ta ce matukar gwamnati ba ta yi wata doka ba cikin wata shida, dakatarwar za ta ci gaba da kasancewa.
Kasashe kamar Pakistan da Bangladesh sun haramta saki uku, amma abin ya ta'azzara a India.
Masu fafutuka sun ce tsarin ya keta 'yancin mace a matsayinta na bil'adam.
Yayin da wasu kungiyoyin musulmi ke cewa haramta sakin take-yanke tamkar yin shisshigi ne cikin harkokin addinai.