Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tuhumi yarinyar da ta kashe 'wanda zai mata fyade'
Wata yarinya 'yar shekara 17 wadda aka ce ta kashe wanda ya nemi ya yi mata fyade za ta gurfana a gaban kotu kan tuhuma kisa bayan ta mika kanta ga 'yan sanda a Afirka ta Kudu.
Ta daɓa mutumin ne mai shekara 21 wuka bayan ta samu galaba a kansa a hatsaniyar da suka shiga a wani kauye da ke arewacin lardin Limpopo, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
'Yan sanda sun ce yarinyar da ake tuhumar, wadda ba ta balaga ba, a dokar Afirka ta Kudu, kuma ba za a iya ambata sunata ba, za ta samu wani jami'in zamantakewa, wata kila da mai ba da shawara da zai taimaka mata a shari'ar da za a mata."
Kanar din 'yan sanda Moatshe Ngoepe ya shiada wa BBC cewar: "A bayanne ya ke cewar hankalinta ya tashi a lokacin da ta isa caji ofis din kuma za ta samu kulawar da ya kamata a irin wannan yanayin."
Akwai rahotannin da suke cewa yarinyar za ta shaida wa kotu cewa matakin da ta dauka na kare kai ne.