Bayanan hoto, A yanzu fasinjoji da ke bin jiragen sama daga Abuja zuwa wasu sassan kasar dama wasu kasashen duniya na tashi ne daga Kaduna a arewacin kasar.
Bayanan hoto, Wakilin BBC Nura Muhammad Ringim ya ce a ranar Alhamis da ya ziyarci filin jirgin Kadunan ana ta hada-hada sosai irin wace ba a saba yi ba a can baya.
Bayanan hoto, Tuni hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya ta gudanar da shirye-shirye wajen daukar matakan kare lafiyar fasinjoji.
Bayanan hoto, An kuma aika 'yan sanda zuwa yankin domin kara tabbatar da tsaro
Bayanan hoto, A yanzu dai za a dinga daukar fasinjojin da suka sauka daga jirgi ne da cikin bas-bas zuwa Abuja, karkashin rakiyar'yan sanda, haka kuma za a dinga dauko masu tafiya daga Abujan zuwa Kaduna.
Bayanan hoto, Gwamnati ta bayar da umarnin rufe filin jirgin saman ne saboda gyare-gyare da za ta yi a filin jirgin saman Abujan.