Yadda Afirka za ta magance labaran bogi

A lokacin da ake ci gaba da fama da labaran karya, wakilin BBC Dickens Olewe, ya duba irin darussan da za a koya daga kafafen yada labaran Afirka. A sharhin da ya yi ya duba wasu labaran bogi da suka yaudari mutane a baya bayan nan:

Labarin cewa:

- An umarci mazan kasar Eritrea su auri mata biyu ko su shiga kurkuku;

- Burtaniya ta ce 'yan Najeriya da wasu kasashen Afirka da ke kungiyar kasashen Commonwealth za su iya shiga kasar ba tare da takardar izini, wato biza, ba.

- Trump ya ce "'Yan Afirka wawaye ne kuma sun cika son jiki, ba abin da suka sani sai ci da jima'i da ta'addanci".

- Robert Mugabe ya ce 'yan Zimbabwe mutane ne masu gaskiya amma sata a cikin jinin duk 'yan Kenya take.

Dickens ya yi bayanin cewa wasu marubutan na yin irin labaran ne saboda su samu mutane da yawa da za su ziyarci shafukansu na intanet.