China ta kaddamar da jiragen yaki masu layar zana

Kasar China ta kaddamar da wasu jiragen yaki biyu da ta kirkiro wadanda suka fi ko wanne fasaha a wani taro a kudancin birnin Zhuhai.

Wadannan Jirage sun dau hankulan manyan baki, da 'yan kallo, da kuma jagororin masana'antu a bikin kaddamarwar.

Jiragen da aka yiwa lababi da J-20 na da wata fasahar da za ta hana iya gano su a duk inda suke.

Don sirri da kuma kare satar fasaha, ba a bai wa mutane izinin kallon jiragen a kasa ba.

Za kuma a yi baje kolin wasu kayan aikin sojin a wani taro mafi girma na kasar ta China.

Wadannan kaya za su hada da na'urorin binciken jirage da kasar ke fatan sayarwa baki 'yan kasashen waje.